Zalunci ne ya jawo talauci da barace-barace a Arewa – Inji Shehu Sani

Zalunci ne ya jawo talauci da barace-barace a Arewa – Inji Shehu Sani

Mun samu labari daga Jaridar Vanguard cewa Sanata Shehu Sani, ya yi magana game da batun talaucin da ake cewa ya yi wa Arewacin Najeriya daurin dabaibayi.

Shehu Sani wanda ya taba wakiltar Mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya ce rashin adalci da sakacin shugababni ya kawo talauci da kuma barace-barace.

‘Dan siyasar ya bayyana cewa rashin shugabanci na-gari ne ya yi sanadiyyar bara da talauci a Yankin Arewa, inda ya ce doka kadai ba za ta shawo kan matsalar ba.

Kwamred ya yi wannan bayani ne a Ranar Alhamis, inda ya nuna rashin goyon bayansa ga dokokin da wasu Gwamnoni su ke yunkuri kawowa domin hana bara.

“An samo baran da ake yi a Yankin Arewacin Najeriya ne a sakamakon talauci, da watsi, da matsalolin zamantakewa, da al’ada da kuma a addini.” Inji Sanata Sani.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda sun gano gidan da ake ajiye kananan yaran jama’a a a Ribas

Zalunci ne ya jawo talauci da barace-barace a Arewa – Inji Shehu Sani
Sanata Sani ba ya ganin haramta bara a Arewacin Najeriya zai yi aiki
Asali: UGC

“’Yan siyasar Arewa su fahimci cewa ba zai yiwu a zauna ba tare da Almajiran da su ka kirkira a shekarun baya ba. Mabarata su na cikin matsalar da su ka haifar.”

Sanatan ya nuna cewa akwai laifin gwamnatocin da aka yi a baya. Sai ya ce: “Ba za ka iya kawo karshen barace-barace ba tare da ganin bayan talauci da jahilci ba.”

Ya ce: “Samar da aikin yi da karfafawa jama’a da kuma taka matsalolin al’adu da rayuwar zamantakewa da su ka jawo bara shi ne abin ya kamata a soma da shi.”

“Wasu Jihohi a shekaru 20 din bayan nan sun yi kokarin hana bara, amma ba su yi basara ba. Sai su yi amfani da Mabarata su ci zabe, bayan zabe kuma su kama su.”

“Kama Mabarata a daure su ya na nufin boye matsalolinmu ne ba shawo kansu ba.” Inji Shehu Sani. Wanann shi ne ra’ayin Sani tun ya na majalisar dattawa a 2015.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel