Yanzu-yanzu: Wani mutum ya sake daka tsalle ya fada ruwa a Legas (Hotuna)

Yanzu-yanzu: Wani mutum ya sake daka tsalle ya fada ruwa a Legas (Hotuna)

Bayan kimanin kwanaki 10 bayan wani mutum ya sauka daga motar haya ya daka tsalle ya fada cikin ruwa a Legas, wani mutum mai matsakaicin shekaru a daren jiya shima ya daka tsalle daga motar haya ta Uber ya fada cikin ruwa a Legas.

Mutumin da a halin yanzu ba a bayyana sunan sa ba ya daka tsalle ya shiga ruwan ne daga gadar Third Mainland a tsakar dare a Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.

The Punch ta gano cewa mutumin da ya daka tsallen ya fada a kan wasu tarin katakai da ke yawo a kan ruwa a karkashin gadar ta Third Mainland.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas

Direban motar ta shaidawa jami'an 'yan sanda na RRS cewa ya dako fasinjan ne daga unguwar Igando da ke wajen birnin Legas.

Ya ce, "Na dauko shi daga Igando kuma ya dage cewa dole in bi ta hanyar gadar Third Mainland.

"Da muka isa gadar sai ya tambaye ni ko nan ne gadar Third Mainland ni kuma na amsa da ce masa eh.

"Ya fada min yana bukatar ya yi fitsari kuma ya bukaci in jira shi a mota ta. Hakan ya janyo hankali ne tunda ya ce in jira shi. Na yi dabara na tuka shi zuwa wurin da jami'an RRS suke tsaye.

"Na fada mishi ba zan kai shi inda zai tafi ba sannan na tafi wurin 'yan sandan na bar shi a cikin motar."

Wani da abin ya faru a gabansa ya ce, "Lokacin da direban ya fara tafiya wurin 'yan sanda domin fada masa abinda fasinjan ya ce, fasinjan ya yi wuf ya fice daga motar kirar Volkswagen Jetta ya daka tsalle cikin ruwa amma ya dira a kan katoko.

"Kafin ya yi tsallen wani dan sanda da ya hange shi ya roke shi kada ya fada ruwan amma ya ki amince wa."

The Punch ta gano cewa an ceto mutumin duk da cewa ya samu rauni daban-daban.

An gano cewar an garzaya da shi asibiti domin yi masa magani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel