NEC: Shugabannin PDP za su yi wani zama na musamman Yau
Shugabannin jam’iyyar PDP za su yi wani zama na musamman a sakamakon taron gaggawar da aka kira wanda za a yi Yau Alhamis a Garin Abuja.
Kamar yadda sanarwar ta nuna, majalisar NEC za ta yi wani zaman gaggawa ne a babban Hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.
A wani gajeren jawabi da babban jam’iyyar hamayyar ya fitar ta bakin Sakatarenta, Umar Tsauri, ta ce za a yi wannan zama ne a Rana 27 ga Fubrairu.
Sai dai a jawabin na Umar Tsauri wanda shi ne babban Sakataren jam’iyyar PDP na kasa bai bayyana dalilin wannan zama da ya taso kwatsam ba.
A sanarwar da aka bada, shugabannin PDP za su zauna a dakin taro ne da karfe 3:00pm. Wannan zai bada dama ga wadanda su ke nesa su halarci taron.
KU KARANTA: Gwamnonin jamm'iyyar hamayya sun sa labule a Najeriya
PDP ta bada wannan muhimmin sanarwa ne kusan a lokacin da gwamnonin jam’iyyar su ke wani taro a babban birnin tarayya Abuja a Ranar Laraba.
Gwamnonin sun gana ne a gidan gwamnan jihar Sokoto da ke Unguwar Asokoro. Shugaban gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ya jagoranci zaman.
A tsarin jam’iyyar PDP, gwamnoni su na cikin wannan majalisa ta NEC, wanda ita ce mafi kololuwar majalisar da ke da ikon zartarwa a jam’iyyar.
A karon baya da PDP ta kira irin wannan taro na NEC, gwamnoni 12 ba su samu halarta ba. Ana sa ran cewa a taron yau, gwamnonin jihohi su iya zuwa.
Watakila zaman da za ayi bai rasa nasaba da shari’ar da ake yi a kotun koli. A Watan Junairu NEC ta zauna ne bayan kotun koli ta ruguza nasarar PDP a Imo.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng