Yanzu-yanzu: An kai wa shugaban APC na jihar Kwara hari

Yanzu-yanzu: An kai wa shugaban APC na jihar Kwara hari

Wasu wadanda ake zargin 'yan daban gwamnan jihar Kwara Gwamna AbdulRazaq sun hari shugaban jam'iyyar APC na jihar Kwara, Bashir Bolarinwa da sauran shugabannin jam'iyyar. Sun kai harin ne a yammacin Talata.

An gano cewa an hari shugabannin jam'iyyar ne a garin Shao da ke karamar hukumar Moro ta jihar, yayin da suka je zagayen godiya ga jama'ar jihar sakamakon goyon bayan da suka basu a zaben da ya gabata.

A yayin harin, motar jam'iyyar da ke dauke da shugabannin jam'iyyar duk an tarwatsa ta, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

An gano cewa hatta gilasan motar sai da aka lalata, wanda hakan ya jawo raunika ga shugaban jam'iyyar na jihar tare da mukarrabansa.

Don tseratar da kai daga harin, 'yan jam'iyyar da magoya bayansu sun tsere don neman mafaka.

Yanzu-yanzu: An kai wa shugaban APC na jihar Kwara hari
Yanzu-yanzu: An kai wa shugaban APC na jihar Kwara hari
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

A yayin harin, 'yan wasu kungiya wadanda magoya bayan gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ne sun fada wajen taron tare da hana shugaban jam'iyyar da mambobin daga yin taron da zasu yi.

A yayin tabbatar da ci gaban, mataimakin shugaban jam'iyyar, Sunday Oyebiyi, ya kwatanta harin da abu mai muni kuma hakan zai iya tarwatsa hadin kan jam'iyyar.

Amma kuma, Gwamna Abdulrazak ya kushe harin da aka kai wa shugaban jam'iyyar na jihar da tawagarsa a Shao. Yayi kira ga jami'an tsaro da su zakulo wadanda suka yi mugun aikin tare da gurfanar dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: