Kujerar gwamnan Bayelsa: Kotun koli ta yi watsi da bukatar Lyon da APC
Kotun koli tayi watsi da bukatar jam'iyyar APC na kara duba shari'ar kwace kujerar gwamnan jihar Bayelsa daga David Lyon da mataimakinsa a jam'iyyar APC.
Kamar yadda mai shari'a Amina Augie ta karanto hukuncin a ranar Laraba, ta bayyana cewa bukatar ba ta da makama kuma hukuncin kotun shi ne madaidaici kuma na karshe.
Ta kara da cewa masu mika bukatar sun kasa bayyana kuskuren, don haka hukuncin ne na karshe a ko ina.
Alkalin kotun kolin ta ce hukuncin ne na karshe kuma babu wata kotu a duniya da za ta iya sauya hukuncin.
DUBA WANNAN: Bayan shekaru 14 da rufe ma'aikata, 'yan majalisa sun gano ana ci gaba da biyanta albashi
Ta kara da cewa wannan bukatar ba ta da amfani kuma wanda ya shigar da wannan bukatar zai biya tarar naira miliyan 10.
Mai shari'a Augie ta kara da cewa lauyoyin APC da na Lyon kowanne zai biya Gwamna Douye Diri da mataimakinsa tare da jam'iyyar PDP naira miliyan 10.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng