Masana su na hasashen takarar Fayemi/El-Rufai a Jam’iyyar APC a zaben 2023
A jiya wasu Masana da masu nazarin harkar siyasan Najeriya su ka yi hasashen cewa Dr. Kayode Fayemi da Malam Nasir El-Rufai ne za su rikewa APC tuta a zaben 2023.
This Day ta ce akwai yiwuwar jam’iyyar APC mai rike da mulkin Najeriya ta tsaida gwamnoni Kayode Fayemi da Nasir El-Rufai a matsayin ‘Yan takara a zaben shugaban kasan.
Rahoton wannan jarida ya bayyana cewa gwamnonin na jihohin Ekiti da Kaduna su na cikin wadanda su ka fi dacewa da mulkin Najeriya idan aka duba halin da ake ciki a yanzu.
Nasir El-Rufai da Dr. Kayode Fayemi su na da duk abubuwan da ake bukata wajen neman kujerar shugaban kasa a Najeriya, kuma ana ganin cewa su na tare da shugaban kasa Buhari.
Bayan kusancin wadannan ‘Yan siyasa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, akwai alamun cewa su na kan shafi daya da wasu manyan Mukarrabai da na-kusa da shugaban kasan.
KU KARANTA: Kujerar Mataimakin Shugaban Jam’iyya ta kai shugabannin APC kotu
Hakan na zuwa ne bayan gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya fara kiran cewa ya kamata mulki ya koma Kudancin Najeriya, inda ake tunanin Jagoran APC Bola Tinubu ya na dako.
Hasashen da wadannan Masana su ka yi, ya nuna cewa Gwamna Fayemi da kuma El-Rufai su na iya doke Bola Tinubu wajen samun tikitin takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.
Gwamna Fayemi wanda tsohon Minista a gwamnatin Buhari zai sauka daga mulkin Ekiti ne a 2022. Shi kuma El-Rufai ya na kan wa’adinsa na biyu a matsayin gwamnan Kaduna.
A halin yanzu wasu Dattawan kasar irin su Tanko Yakassai sun yaba da matsayar gwamna El-Rufai na kiran maida mulki Kudu. Sai dai kuma wasu sun soki gwamnan a kan wannan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng