Hukumar PPPRA ta fatattaki Ma'aikata saboda ta dauki ‘Ya ‘yan Mala’au aiki

Hukumar PPPRA ta fatattaki Ma'aikata saboda ta dauki ‘Ya ‘yan Mala’au aiki

Jaridar Sahara Reporters ta fitar da wani rahoto ta na cigaba da zargin PPPRA da daukar wata daga cikin ‘Ya ‘yan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari aiki a boye.

Sahara Reporters ta ce ta binciko yadda aka dauki Hadiza Muhammadu Buhari aiki a hukumar da ke kula da farashin man fetur na kasa watau PPPRA, ba tare da bin doka ba.

Fadar shugaban kasa ta karyata wannan zargi tun-tuni, inda ta ce babu wata ‘Diyar shugaba Muhammadu Buhari da ke aiki a wannan hukuma da ake ta faman rade-radi.

Sai dai Jaridar Sahara Reporters ta ce ta na nan a kan bakanta, domin har ma ta gano cewa babban Sakataren PPPRA, Abdulkadir Umar Saidu, shi ne ya yi wannan aiki.

A cewar Jaridar Hadiza Buhari ta samu wannan aiki mai tsoka ne ta kafan sabon Sakataren da aka nada a hukumar a 2018, wanda ya sallami ma’aikatan wucin-gadi fiye da 30.

KU KARANTA: Labarin inda 'Ya 'yan Shugaban kasa Buhari su ka yi karatu

Hukumar PPPRA ta fatattaki Ma'aikata saboda ta dauki ‘Ya ‘yan Mala’au aiki
Sahara Reporters ta ce an ba Hadiza Buhari aiki a Hukumar PPPRA
Asali: Instagram

Jaridar ta ce Saidu ya fatattaki Ma’aikata 34 da su ka shafe shekaru bakwai su na aiki da hukumar. An yi wannan ne bayan sun fara sa ran cewa za a ba su aikin din-din-din.

Kafin gwamnatin Najeriya ta nada Saidu a 2018, Misis Sotonye Iyoyo ce wanda ta ke shugabantar wannan hukumar tarayyar, kuma har ta samu iznin daukan mutane 134 aiki.

A maimakon a bada dama ga kowane ‘Dan kasa ya nemi wannan aiki, sai aka dauki ma’aikatan ta karkashin kasa ba tare da an sani ba, daga ciki ne Hadiza Buhari ta samu shiga.

Ana rade-radin cewa Umar Saidu wanda aka ba ikon wannan hukuma ya fito ne daga Garin Daura a jihar Katsina, watau Mahaifar shugaban kasa, sai dai babu tabbacin hakan.

Akwai ‘Yanuwan Saidu da su ka samu aiki a hukumar. Haka zalika an ba ‘Diyar wata Jami’ar EFCC kujera daya. An kuma raba wasu kujeru ga shugabannin kungiyar PENGASSAN.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel