Yanzu-yanzu: Oshiomole, manyan jiga-jigan APC da PDP sun dira kotun yayinda ake shirin sake duba shariar zaben gwamnan jihar

Yanzu-yanzu: Oshiomole, manyan jiga-jigan APC da PDP sun dira kotun yayinda ake shirin sake duba shariar zaben gwamnan jihar

Kotun koli ta shirya tsaf domin sauraron bukatar jamiyyar All Progressive Party APC na sake duba shari’ar zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Jam’iyyar ta bukaci kotun ta janye shari’a da ta yanke na kwace nasara daga hannun dan takarar gwamnan APC, David Lyon.

Shugaban jam’iyyar APC, Adam Oshiomole, gwamnan jihar Bayelsa, Duoye Diri, da sauran jiga-jigan yan siyasan sun dira kotun domin shaida zaman kotun.

Kwamitin Alkalan kotun koli bakwai karkashin jagorancin Jastis Sylvester Ngwuta zai saurari kara.

Lauyan David Lyon, Afe Babalola, ya yi kira ga kotun ta janye shari’ar da ta yanke a ranar 13 ga Febrairu 2020.

Ya bayyana cewa kotun na da idon janye hukuncin da ta yanke saboda an yi cuta da rufa-rufa lokacin yanke hukuncin kuma kotun ba tada ikon yin abinda tayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel