Yaki da ta’addanci: Jiragen Najeriya sun tarwatsa mafakar yan Boko Haram a Borno

Yaki da ta’addanci: Jiragen Najeriya sun tarwatsa mafakar yan Boko Haram a Borno

Hukumar rundunar Sojan sama ta bayyana cewa jiragenta dake yaki da ta’addanci a yankin jahar Borno masu sunan Rattle Snake 3 sun yi aman wuta a kan wasu gine gine da mayakan Boko Haram ke amfani dasu wajen fakewa.

Daily Trust ta ruwaito mai magana da yawun rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace jiragen Rattle Snake suna lalata sansanonin tare da kayayyakin aikin Boko Haram a yankunan Garin Malona da Parisu, duk a cikin dajin Sambisa.

KU KARANTA: PDP ta bukaci kotun koli ta sake nazari game da hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa na 2019

Daramola ya ce a ranar 23 da 24 na watan Feburairu ne Sojojin rundunar Sojan sama dake sarrafa jiragen yakin suka tashi sansanonin biyu a cikin yakin da gwamnatin Najeriya ke yi da yan ta’adda karkashin Operation Lafiya Dole a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

“Mun kai harin ne bayan samun sahihan bayanai dake tabbatar da mayakan Boko Haram da suka kaddamar da hare hare a garin Garkidan jahar Adamawa sun fito ne daga sansanonin a cikin Sambisa

“Wannan ne yasa rundunar Sojan sama ta tura jiragen yakinta don su yi aman wuta a sansanonin tare da lalata dukkanin gine ginen dake cikinsu da kuma kayan aikinsu da makamansu dake jibge a wajen, kuma daga karshe mun hangesu sun kama da wuta duka.” Inji shi.

Daga karshe, ya ce rundunar Sojan sama za ta cigaba da aiki tukuru tare da dakarun Sojin kasa, sa’annan kuma za ta cigaba da rike ma yan ta’adda wuta wajen kai hare hare don tabbatar da an ragargaji Boko Haram gaba daya.

A wani labari kuma, a sakamakon rikicin kabilanci tsakanin makiyaya da manoma wanda ya sabbaba samun hare haren yan bindiga a wasu yankunan kudancin Najeriya, wata kabila dake jahar Delta ta haramta ciniki da cin naman shanu a tsakanin jama’anta.

Jaridar Punch ta ruwaito kabilar Uwheru dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa ce ta dauki wannan tsatstsauran mataki, inda tace ba’a kara sayar da naman shanu ko cin naman shanu a masarautarta don nuna bacin ranta ga hare haren da ta ce makiyaya suna kai ma manomanta da sauran jama’a.

Wannan sabuwar doka da shuwagabannin al’ummar kabilar Uwheru suka kirkiro ya biyo bayan wasu hare hare da suke zargin makiyaya ne suka kai masarautar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel