Mai farin jini: Dubban jama'a sun yi tururuwar fitowa domin tarbar Buhari a Ondo (Hotuna)
A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ziyarci jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya domin ya kaddamar da wasu aiyuka da gwamnatin jihar ta yi.
Takanas jihar Ondo ta bayar da hutun aiki ranar Talata domin zuwan shugaba Buhari wanda ya yi daidai da ranar fara shagulgulan bikin murnar cikar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu, shekaru uku a kan karagar mulki.
Wasu na ganin ziyarar ta shugaba Buhari nada nasaba irin ta siyasa, saboda zata kara wa gwamna Akeredolu, mai neman tazarce a karo na biyu, farin jini wajen sake samun tikitin takarar gwamna a jam'iyyar APC mai fama da rabuwar kayuwa.
DUBA WANNAN: Wata mata ta haifi 'yan tagwaye a layin karbar tallafin gwamnati a Jigawa
Za a gudanar da zaben fidda 'yan takara ne a watan Yuli, kuma tuni 'yan takara masu karfi a jihar suka fara shirye shiryen ganin APC ta kwace takara daga hannun Akreredolu ta mika musu.
Ana ganin cewa Akeredolu zai yi amfani da ziyarar shugaban kasa domin nuna irin nasarorin da ya samu a cikin shekaru uku da ya yi yana mulki.
A cewar kwamishinan yada labaran jihar Ondo, Donald Ojogo, ya ce bayar da hutun aiki a jihar ya zama dole domin karrama shugaba Buhari yayin ziyararsa.
Dandazon jama'a; Maza da Mata, sun yi tururuwar fito wa domin tarbar shugaba Buhari a kan manyan titunan garin Akure, babban birnin jihar Ondo.
Yayin ziyararsa, shugaba Buhari zai kaddamar da muhiiman aiyuka guda biyu; rukunin masana'antu na Ore (Ore Industrial Hub) da katafariyar gadar Ore (Ore Inter-change).
Gwamnatin jihar Ondo ta sanar da cewa kaddamar da aiyukan na daga cikin shagalin murnar cikar gwamnatin Akeredolu shekaru uku a kan mulki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng