Hisbah ta kama wata mata da ke auren maza biyu a Kano

Hisbah ta kama wata mata da ke auren maza biyu a Kano

Wata matar aure mai suna Hawa Kulu mazauniyar unguwar Mariri a jihar Kano ta shiga hannun hukumar Hisbah, bayan an kama ta da laifin auren maza biyu a lokaci daya.

Da farko dai matar na zaune da mijinta na farko ne amma sai ciwo mai hadi da jinya matsananciya ta kama shi. Tuni kuwa ta mayar da shi kauye inda aka ci gaba da jinyarsa.

Bayan dawowarta ta ci gaba da zamanta, sai ta hadu da wani mutum wanda ta sanar da shi cewa ita bazawara ce. Bayan wani lokaci kuwa ya fitar da kudin sadaki aka daura musu aure.

Da yake direbane mijin na biyu, ya kan je nema sannan ya dawo wajen amarya a yi ta soyayya.

Bayan dawowa daga wata tafiya ne suna daki tare sai ga mijin farko ya bayyana tare da kurma ihun cewa kwarto ya shigo masa dakin mata.

Shi kuwa mijin na biyu sai tashi yayi tare da fara tuhumar mijin cewa ya shigo masa gida har daki babu izini.

Hisbah ta kama wata mata da ke auren maza biyu a Kano
Hisbah ta kama wata mata da ke auren maza biyu a Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda yasa NSA Monguno bai halarci taron Buhari da shugabannin hukumomin tsaro ba

A nan kuwa rikici ya balle wanda har ya kai su ga ofishin Hisba da ke yankin karamar hukumar Kumbotso

A bangaren Hauwa Kulu kuwa mai auren maza biyu, ta bayyana cewa mijinta na farko Malam Bello ya sauwake mata, lamarin da Malam Bello ya musanta.

Malam Bala kuwa, wato mijin Hauwa Kulu na biyu ya ce shi kuwa matarsa ce kuma babu wanda zai raba shi da ita.

A halin yanzu ma kuwa suna da yaro daya namiji bayan ya tarar da ita da yara shida na Malam Bello.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel