Wata sabuwa: Kwararrun likitoci sun shiga yajin aikin 'sai baba ta gani', sun bayyana dalili

Wata sabuwa: Kwararrun likitoci sun shiga yajin aikin 'sai baba ta gani', sun bayyana dalili

Kungiyar kwararrun likitoci (MDCAN) ta sanar da shiga yajin aikin 'sai baba ta gani' domin nuna adawarsu da matakain da hukumar kula da jami'o'i ta kasa (NUC) ta dauka a kan cewa sai manyan likitocin sun mallaki digiri na uku kafin su samu cigaba a tsarin jami'a na Najeriya.

Shugaban kungiyar MDCAN na kasa, Farfesa Kenneth Ozoilo, shine ya sanar da hakan yayin wani taro da ya yi da manema labarai a Jos ranar Talata.

Da yake sanar da shiga da yajin aikin, Farfesa Ozoilo, ya umarci dukkan manyan kwararrun likitocin su yi biyayya da kiran uwar kungiya, su shiga yajin aikin.

"NUC ta dauki matakin da ya bamu kunya, ta dauki matakin ne ba tare da yin la'akari da abinda zai biyo baya ba.

"Hakan yasa bamu da wani zabi da ya wuce mu janye aiyukanmu daga jami'o'i ba tare da wani bata lokaci ba," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

iiq_pixel