Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya mutu

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya mutu

Rahoto daga gidan talabijin kasar Misr na nuna cewa Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya rigamu gidan gaskiya.

Hosni Mubarak ya mutu yana mai shekaru 91 a duniya. Ya cika a wani asibitin birnin Alkahira inda akayi masa aikin tiyata.

Ya shugabanci kasar Masar an tsawon shekaru 30.

An kawar da shi daga mulki a shekarar 2011 lokacin zanga-zangar juyin-juya halin da ya mamaye kasashen labarawa a shekaru goma da suka shude.

Tun daga lokacin yake fuskantar rashin lafiya da kuma gurfana a kotu.

Mubarak ya jagoranci kasar Masar daga 14 ga Oktoban 1981 zuwa 11 ga Febrairun 2011. Gabanin hakan, ya kasance mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1975 zuwa 1981, sannan ya zama Firam Ministan Masar daga 1975 zuwa 1981.

Ya mutu ya bar jikoki hudu, Omar Alaa Mubarak, Mahmoud Gamal Mubarak, Farida Gamal Mubarak, da Mohammed Mubarak.

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya mutu
Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya mutu
Asali: UGC

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya mutu
Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Masar, Hosni Mubarak, ya mutu
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel