Bayelsa: DSS ta karyata zargin kama yaran Shugaban alkalan Najeriya su 2
- Rundunar tsaro na farin kaya wato DSS ta karyata zargin kama yaran Shugaban alkali Najeriya, Sirajo da Sanni Tanko
- Hakan martani ne ga rahoton wata jaridar yanar gizo da ke cewa jami’an DSS ta kama yaran Shugaban alkalan biyu
- Kafar labaran ta yi ikirarin cewa wani tsohon hadimin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda aka sakaya sunansa ne ya fallasa labarin a Twitter
Rundunar tsaro na farin kaya wato DSS ta karyata zargin kama yaran Shugaban alkali Najeriya, Sirajo da Sanni Tanko.
Wata jaridar yanar gizo, Observers Times, ta ruwaito a ranar Litinin cewa jami’an DSS ta kama yaran Shugaban alkalan biyu.
Kafar labaran ta yi ikirarin cewa wani tsohon hadimin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda aka sakaya sunansa ne ya fallasa labarin a Twitter.
Sai dai kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya ce: “ba a kama su ba, ba mu kama yaran Shugaban alkalan Najeriya guda biyu ba.”
Rahoton ya ce hadimin tsohon Shugaban kasar ya tabbatar da cewar an kwace wayoyinsu sannan aka bincika dukkanin sakonni da kiraye-kirayen da aka yi a wayoyin.
Rahoton ya yi ikirarin cewa an saki daya daga cikin yaran biyu kan beli yayinda dayan ke a hannun DSS a safiyar Litinin.
Har ila yau rahoton ya alakanto tsohon hadimin na cewa an kama su ne domin barazana ga Shugaban alkalan kasar don ya janye hukuncin da kotun koli ta yanke kwanan nan a jahar Bayelsa.
“Yana daga cikin shirin razana kotun koli domin ta janye hukuncin zaben Bayelsa ta yadda jam’iyyar All Progressives Congress za ta haye,” kamar yadda aka rahoto tsohon hadimin na fadi.
KU KARANTA KUMA: Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya mutu yana da shekara 112
Ku tuna a farkon watan nan ne kotun koli ta tsige dan takarar APC a jahar Bayelsa kuma zababben gwamna, Mista David Lyon sannan ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta da ta bayar da shahadar cin zabe ga Sanata Diri Duoye na jam’iyyar Peoples Democratic Party.
Kotun kolin ta riki cewa abokin takarar Lyon, Biobarakuma Degi-Eremienyo, ya gabatarwa da INEC bayanan karya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng