Ya dace a hada da matasan Fulani cikin rundunar Amotekun – Miyetti Allah

Ya dace a hada da matasan Fulani cikin rundunar Amotekun – Miyetti Allah

Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Oyo, Alhaji Yakubu Bello ya yi kira da a saka yan Fulani a cikin kungiyar tsaro ta musamman da gwamnatocin jahohin yarbawa ta kirkiro don kare yankin mai suna Amotekun.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Bello ya bayyana haka ne yayin taron sauraron ra’ayoyin jama’a game da kudurin dokar kafa rundunar Amotekun daya gudana a majalisar dokokin jahar Oyo a ranar Litinin.

KU KARANTA: Mai dokar barci ya buge da gyangyadi: An kama Dansanda da laifin sata da garkuwa da mutane

A jawabinsa, Bello ya ce ba dukkanin bafulatani bane mutumin banza, kuma mutumin banza ne kadai yake tsoron kafa sabuwar hukumar tsaro, shi yasa ya bukaci a sanya Fulani a rundunar, don haka ya bayyana goyon bayansa ga yunkurin kafa rundunar Amotekun.

Shi ma a nasa jawabin, Kaakakin majalisar dokokin jahar Oyo, Adebo Ogundoyin ya bayyana muhimmancin kafa rundunar Amotekun, saboda a cewarsa za ta taimaka ma rundunar Yansnda wajen kare rayuka da dukiyar jama’a.

“Za’a samar da Amotekun ne don taimaka ma hukumomin tsaro wajen shawo kan matsalolin tsaro dake addabar yankin Yarbawa. Mu ma a majalisar dokokin jahar Oyo ta 9 mun tashi haikan don tabbatar da shi, shi yasa muka gayyato jama’a don su bada gudunmuwarsu ga kudurin doka.” Inji shi.

A jawabinsa, hadimin gwamnan jahar Oyo a kan harkar tsaro, Fatai Owoseni ya bayyana cewa rundunar Amotekun ba za ta sanya karar tsana a kan wata kabila ko addini ba, amma za ta tabbatar da zaluko duk wasu miyagun mutane a duk inda suke.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki ta yini guda jahar Ondo domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jahar ta kammala a karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu SAN.

Gwamna Rotimi da kansa tare da manyan jami’an gwamnatinsa ne za su tarbi shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yan tawagarsa, inda shugaban zai kaddamar da wani katafaren gadar sama da cibiyar masana’antu a garin Ore, na karamar hukumar Odigbo.

Ana sa ran jagoran jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu na daga cikin wadanda zasu raka shugaba Buhari zuwa Ondo, kafatanin gwamnonin jahohin yarbawa 6, ministoci daga yankun Yarbawa da kuma yan majalisu daga jahar Ondo duk zasu halarci taron.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel