Wata sabuwa: Dan luwadi ya fito takarar shugabancin kasar Amurka
- Pete Buttigieg dan takarar shugabancin kasar Amurka ne a zaben da ke gabatowa a watan Nuwamban wannan shekarar
- Idan Buttigieg ya hau mulkin kasar, zai kafa tarihin zama dan luwadi na farko da ya fara zama shugaban kasar Amurka
- Pete Buttigieg ya auri namiji a 2018 amma sai ya ci karo da wata tambaya daga yaro mai shekaru 9 yayin da ya fita gangamin yakin neman zabe a ranar Lahadi da ta gabata
Dan luwadin mai takarar shugabancin kasar Amurka, Pete Buttigieg ya ba wani yaro mai shekaru 9 amsa wanda ya zo taron gangamin siyasa. Yaron ya tambayi dan takarar ne yadda zai bayyana kan shi a matsayin dan luwadi, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.
A ranar Lahadi ne Pete Buttigieg ya hadu da wani yaro mai shekaru 9 yayin gangamin yakin neman zabenshi. Yaron ya tambayi yadda zai sanar da duniya cewa shi dan luwadi ne amma ya kasa.
Buttigieg wanda ya auri namiji, zai zama shugaban kasa na farko dan Luwadi a Amurka idan aka zabe shi a watan Nuwamba. Dan takarar na fita gangamin zaben tare da mijin shi mai suna Chasten Buttigieg wanda ya aura a 2018.
KU KARANTA: Na gwammace sayar da ruwan leda dana dinga zina ana biyana - Cewar wata dalibar jami'a
A ranar Lahadi ne a birnin Colorado Buttigieg ya fuskanci tambayoyi daga jama'a kuma ya amsa.
Yaron mai shekaru 9 ya ce 'Ina son sanar da duniya cewa ni dan Luwadi ne amma ban san yadda zanyi ba'. Bayan kammala karanta tambayar, Buttigieg ya kira yaron har zuwa kan mumbarin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng