Babban dan majalisar dokoki ya sha matsa a hannun jami'an EFCC a Kano
- Hukumar EFCC a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, ta cika hannunta da Shugaban marasa rinjaye kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jahar, Isiyaku Ali Danja
- Ana zargin sa da cin mutuncin kujerarsa da kuma almundanan kudaden da ya kamata ayi ayyukan mazaba da su
- Za a gurfanar dashi a gaban kotu da zaran an kammala bincike
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa reshen jahar Kano, a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, ta gasa Shugaban marasa rinjaye kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jahar, Isiyaku Ali Danja kan zargin cin mutuncin kujerarsa da kuma almundanan kudaden da ya kamata ayi ayyukan mazaba da su.
An fara ja-in-jan ne bayan hukumar ta samu wani korafi cewa an karkatar da kudaden da ya kamata gwamnatin jahar Kano ta biya na haraji zuwa asusun kudaden shiga na tarayya daga asusun jahar Kano.
A yayin bincike, sai aka gano an biya wasu kudade da ke da ayar tambaya zuwa asusun wasu mutane ciki harda kamfanin Allad Drilling Limited, wace ta ke mallakar wanda ake tuhumar.
An kuma gano cewa wanda ake tuhumar ya cire wadannan kudade a lokuta mabanbanta.
Kuma dama shine ya kamata ya tabbbatar da cewar an yi ayyukan kafin a biya kowani kudi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa har yanzu ana kan gudanar da bincike domin gano wadanda suka ci moriyar kudaden da aka fitar daga baitul malin jahar wanda aka ce ya tasar ma naira biliyan 1.4.
KU KARANTA KUMA: PDP ta nemi a sake duba hukuncin kotun koli kan zaben Buhari
Za a gurfanar dashi a gaban kotu da zaran an kammala bincike.
A wani labari na daban, mun ji cewa wata mata mai suna Hadiza Bello tare da abokanta guda uku sun gamu da hukuncin daurin shekaru 160 a gidan gyaran halayya biyo bayan kamasu da aka da laifin damfara da kudin bogi, inji rahoton Punch.
Majiyarmu ta ruwaito babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Yola na jahar Adamawa ne ta yanke musu wannan hukunci bayan hukumar yaki da rashawa da makamanta laifuka, ICPC, ta gurfanar dasu a gabanta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng