Labari da dumi-dumi: Tattalin Najeriya ya motsa da 2.27% a 2019 - NBS
A yau, Litinin, 24 ga Watan Fubrairun 2020 mu ka samu labari cewa karfin tattalin arzikin Najeriya ya motsa da fiye da 2.27% a karshen shekarar da ta wuce.
Alkaluman da hukumar NBS ta fitar a farkon makon nan ya tabbatar da cewa idan aka kamanta da shekara bara, tattalin Najeriya ya motsa ne da kashi 2.55%.
Wannan habaka da tattalin arzikin Najeriya ya yi a karshen bara shi ne mafi bunkasar da tattalin kasar ya yi tun da Najeriya ta farfado daga matsin tattali a 2016.
Hukumar NBS mai alhakin tara alkaluma a Najeriya ta ce an samu karin 0.17% a habakar da tattalin arzikin kasar ya samu daga shekarar 2018 zuwa 2019.
Jawabin hukumar ya ce: “Bunkasar da tattalin arzikin Najeriya ya yi a karshen 2019, ya nuna mafi karfin motsawar da tattalin kasar ya yi tun shekarar 2016.”
KU KARANTA: Za a kara kudin wutan lantarki a Najeriya - Hukumar TCN

Asali: Twitter
“A jimilla, tattalin arzikin Najeriya ya motsa da 2.27% a 2019. A 2018 tattalin arzikin ya motsa ne da 1.91%.” Najeriya ta zarce burin da aka ci mata a karshen bara.
"Jimillar karfin tattalin arzikin na Najeriya watau GDP a karshen shekarar 2019 ya tsaya ne a kan N39, 577, 340. 04. Wannan ya nuna an samu cigaba a kan 2018."
"N35,230, 607. 63 shi ne karfin GDP na kasar a 2018. Idan aka yi la’akari da alkaluman shekara-shekara, za a fahimci cewa tattalin kasar ya habaka da 12.34%."
Hukumar IMF ta yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai motsa ne da 2.1% a karshen bara. A karshe tattalin kasar ya bada mamaki inda ya bunkasa da 2.27%.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng