Abinda ya hana mu bude wa mayakan Boko Haram wuta yayin harin Garkinda - NAF

Abinda ya hana mu bude wa mayakan Boko Haram wuta yayin harin Garkinda - NAF

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta ki bude wa mayakan kungiyar Boko Haram wuta yayin harin da suka kai garin Garkinda na karamar hukumar a Gombia jihar Adamawa saboda gudun kashe fararen hula marasa laifi.

Mazauna garin sun zargi dakarun rundunar sojin sama da kin kawo musu agaji yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari garin a makon da ya gabata.

Da ya ke mayar da martani a kan zargin, Ibikunle Daramola, kakakin rundunar NAF, ya ce akwai karin bayani a kan dalilin da yasa basu bude wa mayakan wuta ko sakar musu bama bamai ba.

Ya ce ba za a zargi rundunar NAF da nuna sakaci wajen tura jiragenta zuwa wurin da aka kai harin ba bayan samun rahoto.

"Akwai bukatar samun bayanai daga sojojin da ke yaki a kasa da wadanda suke cikin jirgi duk da nisan da ke tsaninsu. Sadarwar ta zama dole domin gani cewa ba saki makami a kan fararen hula ko rundunar soji ba.

"A ranar da aka kai harin, 21 ga watan Fabrairu 2020, jama'ar garin sun shiga rudani, a saboda haka akwai mutane da nisa ba zai bari jirgin da ke sama ya tantance mayakan Boko Haram da fararen hula da ke gudun neman mafaka ba," a cewarsa.

Abinda ya hana mu bude wa mayakan Boko Haram wuta yayin harin Garkinda - NAF
Abinda ya hana mu bude wa mayakan Boko Haram wuta yayin harin Garkinda - NAF
Asali: Twitter

Daramola ya cigaba da cewa, "wani abu da ya kara dagula lamarin shine an kai harin ne da daddare. Bisa tsari da dokokin aikin soja na kasa da kasa, ba a kai wa 'yan ta'adda hari da daddare matukar ba tabbatar wa aka yi babu marasa laifi a wurin ba."

DUBA WANNAN: 'Ku tsammani yaki ba kakkauta wa' - Buhari ya yi magana a kan Boko Haram

Kakakin ya kara da cewa rundunar NAF ta kai hari tare da lalata sansanin mayakan da suka kai harin.

Ya ce sun kai harin ne ranar 23 ga watan Fabrairu a maboyar mayakan da ke Parisu a dajin Sambisa.

Kazalika, ya bayyana cewa nan bada dadewa ba rundunar NAF za ta saki bidiyon harin da ta kai maboyar mayakan domin jama'a su gani da idonsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel