Ku shiryawa karin farashin kudin wutar lantarki - TCN

Ku shiryawa karin farashin kudin wutar lantarki - TCN

Kamfanin watsa wutar lantarkin Nigeria ta sanar da yan Nigeria dasu shirya da karin kudin wutar lantarki na daga watan Afrilu domin samun walwalar wutar.

Darakta manaja na kamfanin watsa wutar lantarki TCN, Usman Mohammed, ya bayana hakan ranar Alhamis, yace gwamnati ta cigaba da sanya kudinta a bangaren wutar lantarki duk da bata bayyana hakan ba na tsawon shekaru shida da suka wuce.

Mohammed ya bayyana hakan ne yayin gyara wasu tsofaffin wayoyin watsa wutar lantarki da suka tsinke a karamar hukumar Alimosho-Ogba-Alausa-Ota dake birnin Ikeja.

Yace, “Muna aiki ne domin kamfanin watsa wutar lantarkinmu ta zama itace wadda tafi kowanne kamfani a duniya. Amma inaso in sanarwa yan Nigeria cewa hakan ba zai yiyu ba sai sun biya kudin wuta.

“Ina so in sanar da yan Nigeria cewa ba alaka tsakanin talauci da biyan kudin wutar lantarki.”

Ya kara da cewa Nigeria tafi kowace kasa saukin kudin wutar lantarki a nahiyar Afrika ta yamma.

KU KARANTA Hukumar NAFDAC ta gargadi yan Najeriya kan zuwa teburin Maishayi`

Ku shiryawa karin farashin kudin wutar lantarki - TCN
Ku shiryawa karin farashin kudin wutar lantarki - TCN
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe kimanin tiriliya biyu cikin shekaru uku da suka gabata domin inganta wutan lantarki a Najeriya, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya laburta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan taron kwamitin tattalin arzikin Najeriya a Abuja.

El-Rufa'i ya ce lamarin wutar lantarkin Najeriya ya gurbace gaba daya kuma gwamnatin Buhari ba zata iya cigaba da kashe kudi haka ba.

Yace: "Gaba daya sashen (wutan lantarki) ya kareraye, yadda aka sayar da kamfanin wutan ni ciwa da dama tuwo a kwarya. Saboda haka akwai matsaloli da yawa."

"Abinda mukayi ittifaki akai shine akwai babban matsala a samar da wutan lantarki......Gwamnatin tarayya ta taimakawa bangaren wutan lantarki da N1.7 Trillion a shekaru uku da suka gabata kuma ba za'a iya cigaba da hakan ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel