Da duminsa: Firam Ministan Malaysiya, Mahathir Mohamad, yayi murabus

Da duminsa: Firam Ministan Malaysiya, Mahathir Mohamad, yayi murabus

Firam Ministan Malaysiya, Mahathir Mohamad, ya sanar da murabus dinsa daga kujerar domin bada damar da samar da sabuwar gwamnati.

Ya aikewa sarkin Malaysiya wasikar ne a ranar Litinin misalin karfe 1 na rana (Agogon Malaysiya), jawabi daga ofishin firam ministan ya bayyana.

Jima kadan bayan hakan, ya sake murabus matsayin shugaban jamiyyar Parti Pribumi Bersatu Malaysia (Bersatu).

Murabus din Mahathir Mohamed ya baiwa mutane mamaki kuma hakan ya faru ne bayan an fara rade-radin cewa yana kokarin kafa sabuwar gwamnati tsakanin United Malays National Organisation (UMNO), Parti Islam Se-Malaysia (PAS) da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel