Biliyoyin kudin da Aliko Dangote ya sa a ANAMMCO ya cece mu – Nneji

Biliyoyin kudin da Aliko Dangote ya sa a ANAMMCO ya cece mu – Nneji

A cikin shekaru biyar da su ka wuce, Alhaji Aliko Dangote ya zuba kudin da su ka haura Naira biliyan 63 a cikin kamfanin nan na ANAMMCO masu kera manyan motoci.

Mai kudin Nahiyar Afrikan ya saye manyan motoci na gingimari fiye da 3, 500 a hannun wannan kamfani na 'Anambra Motor Manufacturing Company' watau ANAMMCO.

A shekarar 2016 Aliko Dangote ya shiga yarjejeniya da kamfanin harkar motoci da zirga-zirga na TSS, wannan kamfani ya na karkashin kamfanin sufurin nan na ABC ne.

Daga lokacin da aka sa hannu a kan wannan yarjejeniya zuwa yanzu, Aliko Dangote ya karbi manyan motoci 3, 500 ta hannun kamfanin ANAMMCO da ke Garin Enugu.

Dangote ne wanda ya fi kowa yi wa wannan kamfanin Najeriya masu hada motoci ciniki. A 1980 gwamnatin tarayya ta hada-kai da kamfanin Mercedes Benz ta kafa kamfanin.

KU KARANTA: Ina 'Dan shekara 8 kacal a Duniya na zama Maraya - Dangote

Biliyoyin kudin da Aliko Dangote ya sa a ANAMMCO ya cece mu – Nneji
Aliko Dangote ya sa ANAMMCO sun kera masa motoci fiye da 3000
Asali: UGC

Shugaban kamfanin TSS, Frank Nneji, ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa cinikin da Aliko Dangote ya yi masu ne ya taimaka masu su ka dawo aiki da karfinsu a halin yanzu.

Dangote ya zabi wannan kamfani ya kera masa motocin da ya ke amfani da su wajen hada-hadar kayan kasuwancinsa a maimakon ya shigo da motocin daga kasashen waje.

Wannan ciniki da Attajirin ya ke yi wa kamfanin ya taimaki tattalin arzikin Yankin Kudu maso Gabashin kasar har ta kai ANAMMCO sun babbako da dayan tasharsu a Onne.

Nneji ya shaidawa Manema labarai cewa kamfanin Dangote su ka saye 90% na motocin da su ka kera. A na su bangaren, kamfanin Dangote sun ji dadin wannan yarjejeniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel