Fayose ya yi fatali da batun komawarsa cikin jam’iyyar APC

Fayose ya yi fatali da batun komawarsa cikin jam’iyyar APC

Tsohon gwamnan jahar Ekiti, Ayodele Fayose ya musanta jita jitan da ake yayatawa a kan wai zai fice daga jam’iyyar adawa ta PDP ya wankan tsarki zuwa jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC.

Jaridar BluePrint ta ruwaito mai magana da yawunsa, Lere Olayinka ne ya bayyana haka a madadin Fayose, inda yace mai zai yi da APC, jam’iyyar da ta kamu da cutar Coronavirus? Don haka yace APC ba irin jam’iyyar da mutum kamarsa zai iya shiga bane.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Kaduna ta kalubalanci hukuncin kotu na sakin yan shia 92

Wannan raddi ya biyo bayan maganar da jam’iyyar APC reshen jahar Ekiti ta yi ne, inda ta bayyana cewa Fayose ba shi da kimar da za su amsheshi a cikin jam’iyyarsu, don haka Fayose yace: “Abin dariya ne yadda jam’iyyar APC a Ekiti take karya, kuma take karyata kanta.

“Yanzu haka Fayose yana cikin ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a gidan Sanata Clement Awoyelu dake cikin garin Ekiti. Don haka labarin Fayose zai fit daga PDP zuwa APC karya ne daga jam’iyyar APC.

“Menene abin sha’awa game da APC da zai ja hankalin Fayose cikinta? Kashe kashen da ake yi da satar mutane a duk fadin kasar? Ko kuwa tarin bashin da ta ciyo ma Najeriya? Ko kuwa gwamnatin jaha mara alkibla da ta sallami ma’aikata 3,000?” Inji shi.

Ya karkare da cewa: “Menene abin sha’awa a cikin jam’iyyar APC a nan da har Fayose zai rudu da ita, Fayose wanda aka sansa wajen tsayawa a kan bukatar talaka wanda a yanzu suke shan wahalar gwamnatin APC?”

Daga karshe ya nemi APC ta cigaba da bankaura a kan Fayose yayin da shi kuma zai cigaba da gina jam’iyyar PDP ta yadda zata kwace mulkin jahar a zaben shekarar 2022.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Ebonyi, David Umahi ya sallami wasu hadimansa guda biyu biyo bayan zarginsu da ake yi da aikata laifin kisan kai a yayin zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na zaben shuwagabannin kananan hukumomin jahar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito bugu da kari Gwamna Umahi ya mika mutanen biyu ga hannun hukumar Yansandan Najeriya reshen jahar Ebonyi domin su gudanar da cikakken bincike a kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng