Tsami da wari: Gwamnati ta bayar da umarnin rufe wata cibiyar waraka a Katsina

Tsami da wari: Gwamnati ta bayar da umarnin rufe wata cibiyar waraka a Katsina

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bada umarnin rufe wani gidan maganin gargajiya da ke Tashar Wali a karamar hukumar Dutsi ta jihar Katsina.

Gwamnan ya bada umarnin ne bayan wata ziyarar ba-zata da ya kai cibiyar a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa karamar hukumar Daura.

A take kuwa Gwamna Masari ya ba kwamshinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya, Ya'u Gwojo-Gwoho umarnin kiran shugaban al'amuran karamar hukumar don jin ta bakin mamallakin cibiyar, Sada Salihu.

Bayan gwamnan ya dau lokaci wajen zagaya gidan, ne ya tarar da tsananin kazantar wajen wacce ta matukar girgiza da halin kazantar da ya gani.

Tsami da wari: Gwamnati ta bayar da umarnin rufe wata cibiyar waraka a Katsina
Tsami da wari: Gwamnati ta bayar da umarnin rufe wata cibiyar waraka a Katsina
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwamiti a majalisar wakilai ya yi wa wasu ministoci 4 kiran gaggawa

A tattaunawar da gwamnan yayi da mai cibiyar warakar, ya jaddada cewa warin da ke fitowa daga dakunan ya biyo bayan tsumin rubutun da ake yi ne gidan.

Kamar yadda mai cibiyar ya sanar, ana amfani da ruwan ne wajen wanke jiki, yayin da mata ake basu don su sha don samun waraka.

Amma kuma sai gwamnan ya hanga tare da gano cewa mutanen da ke zuwa karbar magani gidan zasu iya harbuwa da wasu cutuka tunda ko bayi babu a farfajiyar gidan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel