Sanatoci sun yi Allah-wadai da kudirin neman kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun ‘yan Boko Haram

Sanatoci sun yi Allah-wadai da kudirin neman kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun ‘yan Boko Haram

Rahotanni sun kawo cewa wasu daga cikin sanatoci a majalisar dokokin tarayya sun yi Allah-wadai tare da nuna rashin amincewar su da kudirin da Sanata Ibrahim Gaidam ya gabatar, inda ya nemi a kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun yan ta’addan Boko Haram.

A cewar su wannan kudiri da sanata Gaidam ya gabatar a Majalisar Dattawar asarar kudi ne kawai za a yi, sannan cewa hakan bai ma dace ba.

Baya ga haka, sanatocin sun ce su na kokwanton cewa mafi akasarin ‘yan ta'addan na Boko Haram ba ma ‘yan Najeriya ba ne, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci sun yi Allah-wadai da kudirin neman kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun ‘yan Boko Haram
Sanatoci sun yi Allah-wadai da kudirin neman kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun ‘yan Boko Haram
Asali: UGC

Kadan daga cikin abin da kudirin ya kunsa, akwai kokarin saisaita tubabbu, gyara dabi'unsu, sama masu sana’o’in sake rayuwa a cikin al’umma, warware musu mummunar akida, yin afuwa ga wadanda suka ajiye makaman su da sauran su.

Sanata Ago Akinyilure daga Jihar Oyo, ya ce wannan kudiri ba tunani ne mai kyau ba, inda ya kara da cewa mugu dai sunansa mugu.

Sai ya bada shawarar cewa har gara ma a yi amfani da kudin a gyara wuraren da Boko Haram suka lalata.

KU KARANTA KUMA: Yanzun-nan: An tabbatar da mutuwar hazikin soja daya a harin da Boko Haram ta kai Garkida

A nashi bangaren, Sanata Danjuma Laah daga Kaduna ta Kudu, ya ce sam bai amince da hakan ba, inda ya ce an sha kama yan kunar bakin wake a cikin sansanin masu gudun hijira, wadanda a cikinta suke rayuwa.

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar Sojojin Saman Najeriya (NAF) a jiya ta ce ta kashe wasu muhimman shugabannin kungiyar slamic State of West Africa Province (ISWAP) a Jubillaram da Alinwa a arewacin Borno.

Wannan na zuwa ne bayan da dakarun sojojin Operation Hadarin Daji a Zamfara suka kashe 'yan bindiga 13 kuma suka kama wasu takwas a jihar Zamfara.

Direktan watsa labarai na NAF, Ibikunle Daramola a jiya a Abuja ya ce dakarun mayakan sama (ATF) na Operation Lafiya Dole karkashin atisayen Operation Rattle Snake III sun kai wa shugabanin ISWAP hari a lokacin da suka hadu wurin taro bayan samun bayannan sirri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel