Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari

Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa za a fuskanci yaki da Boko Haram babu kama hannun yaro a cikin makonni kadan masu zuwa.

A takardar da mai bada shawara a kan yada labarai, Garba Shehu ya fitar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kushe harin da ‘yan ta’addan suka kai garin Garkida da ke jihar Adamawa. Ya kara da jajantawa iyalan wadanda lamarin ya ritsa dasu.

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya sanar da cewa Boko Haram din ba zasu damar shigowa ba ballantana su kwace wasu sassa na kasar nan ba, yayin da yake mulki ballantana su kafa daularsu.

Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari
Nan da makonni kadan Boko Haram zasu zama tarihi - Buhari
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kwamiti a majalisar wakilai ya yi wa wasu ministoci 4 kiran gaggawa

“Wadannan hare-haren da suke kawowa na nuna alamun damuwa ne da matsin da mulkina yayi musu. Yana bayyana taushin mayakansu ta yadda ba zasu iya shigowa Najeriya a kyalesu ba. Sojinmu sun cancanci jinjina ta yadda suke korarsu. Suna da goyon bayanmu dari bisa dari don ci gaba da yakar ‘yan ta’addan” cewar takardar.

Idan zamu tuna, a jiya Asabar ne 'yan ta'addan Boko Haram din suka kai hari a Garkida da ke jihar Adamawa.

A harin nasu kuwa sun samu damar kona wuraren bauta, ofishin 'yan sanda da sauransu. Sun dau sa'o'i shida suna barnar a cikin garin wanda hakan ya jawo rasa rayuka da kadarori da aka yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel