Malami ya bayyana hanyar shawo kan rikicin manoma da makiyaya

Malami ya bayyana hanyar shawo kan rikicin manoma da makiyaya

- Antoni Janar din kasar nan, Abubakar Malami ya bayyana cewa akwai bukatar shawo kan rikicin manoma da makiyaya a kasar nan

- Ministan shari'ar ya sanar da hakan ne a ranar Asabar kamar yadda takardar da ta fito daga ofishinsa ta bayyana

- Ya ce dole ne a saka manyan dabaru tare da saka masu ruwa da tsaki wajen gyara dabarun ilimantar da fulani makiyaya

Ministan shari’a na Najerriya, Abubakar Malami, SAN yace rikicin manoma da makiyaya a kasar nan yana bukatar dabara ne wajen shawo kan sa, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Antoni Janar din ya sanar da hakan ne a ranar Asabar kamar yadda takardar da ta fito daga ofishinsa ta fito. Yayi kira ga masu ruwa da tsaki a kan su mayar da hankali wajen shawo kan matsalar manoma da makiyaya a kasar nan.

Malami ya bayyana hanyar shawo kan rikicin manoma da makiyaya
Malami ya bayyana hanyar shawo kan rikicin manoma da makiyaya
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar nan

“Zai fi kyau idan aka saka dabara wajen shawo kan rikicin manoma da makiyayya ta hanyar saka masu ruwa da tsaki tare da tabbatar da dabarun hakan. Rashin sasantasu ne zai zama babban kalubale ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya,” ministan ya ce.

Ya kara da cewa, kara duba yanayi tsarin ilimi Fulani makiyaya da kuma kokarin gwamnati zai iya shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel