Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji

Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji

- A shirin da Donald Trump shugaban kasar Amurka yake yi na ziyartar kasar India a mako mai zuwa, wani mutumi ya roki hukumomi a kan ya cika burin shi

- Kamar yadda Bussa Krishna mai shekaru 37 ya bayyana, yayi mafarkin Donald Trump ne kuma sai ya gina gunkinshi wanda yake bautawa

- Krishna ya bayyana cewa soyayyar da ke tsakanin shi da Trump irin soyayya ce da ke tsakanin Ubangiji da bawan shi

Kafin zuwan shugaban kasar Amurka kasar India a mako mai zuwa, wani mutum dan kasar India ya bukaci hukumomi da su tallafa masa cika burin shi na rayuwa na ganin Donald Trump.

Bussa Krishna mutum ne mai shekaru 37 kuma ya hada wata gunkin Trump mai matsakaicin girma a lambunshi wanda yake bautawa.

Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Asali: Facebook

Bussa Krishna ya ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ne Ubangijinsa, kuma ya fara bauta mishi ne tun a shekaru hudu da suka gabata bayan yazo mishi a mafarki.

Bayan mafarkin shi, Krishna ya ce yayi hayar leburori 15 ne wadanda suka yi aikin gina gunkin mai tsayin kafafu 6 na Trump a kauyensu da ke Kudancin Telangana a India.

Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Asali: Facebook

“A maimakon in fara bautar wani ubangiji, na fara bauta mishi,” Bussa Krishna ya sanar da gidan talabijin na New Delhi, yayin nuna musu gunkin Trump da ke sanye da kaya na alfarma. Yana kiran gunkin da “Ubangijina, Donald Trump.”

“Kaunar da ke tsakanina da shi ta koma ta tsakanin Ubangiji da wanda ke bauta mishi. Wannan na kara min farin ciki ba kadan ba. Amma kuma ina fuskantar kalubale daga ‘yan uwana,” Krishna ya ce.

KU KARANTA: An gano coci da ake daukar yara kanana ana koya musu karuwanci a jihar Osun

Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, Krishna ya ce “Suna cewa ina tozarta kaina. Na sanar dasu cewa kamar yadda kuka yarda kuma kuke bautawa Shiva, nima haka na yadda nake bautawa Trump. Babu daya daga cikinmu da zai iya hana daya bautarshi.

"Tamkar Ubangiji yake gareni, hakan ne dalilin da yasa na gina gunkin shi. A kowacce ranar Juma’a ina azumi don fatan tsawon rayuwa ga Trump. Ina duba hoton shi tare da yin addu’a gareshi kafin in fara aiyukana. Trump, kaine Ubangijina kuma ina maka barka da zuwa India. Ina matukar farin ciki.”

Krishna wanda yake rayuwar shi kadai, an san shi a yankin yanzu da Trump Krishna kuma ana kiran gidan shii da gidan Trump.

Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Bussa Krishna: Mutumin da ya dauki shugaban kasar Amurka Donald Trump a matsayin ubangiji
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel