An yi artabu tsakanin Yansanda da yan fashi a Abuja, 2 sun bakunci lahira

An yi artabu tsakanin Yansanda da yan fashi a Abuja, 2 sun bakunci lahira

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja sun samu nasarar tarwatsa wasu gungun miyagun yan fashi da makami a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito an yi musayar wuta tsakanin Yansanda da Yan fashin ne a unguwar Dawaki na Abuja, inda Yansanda suka samu nasarar halaka guda biyu daga cikinsu.

KU KARANTA: Amurka ta haramta ma Najeriya mika $100m daga kudin Abacha ga gwamnan jahar Kebbi

Mai magana da yawun rundunar Yansandan Abuja, Ajuguri Manzah ya sanar da haka a Abuja, inda yace yan fashin sun fuskanci Yansanda ne a daidai inda suka gudanar da fashinsu, wanda hakan ya janyo musayar wuta a tsakanin bangarorin biyu.

“Biyo bayan amsan kiran da Yansanda suka yi zuwa inda miyagun suke fashi, sai yan fashin suka fara neman hanyar tsira, don haka suka shiga harbe harben mai kan uwa da wabi, tare da cinna ma wata katifa wuta da nufin janye hankalin Yansanda.

“A yayin musayar wutan ne Yansanda suka bindige guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere dauke da raunukan bindiga a tare dasu, daga bisani aka garzaya da wadanda aka kama zuwa asibiti, inda a can likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.” Inji shi.

DSP Manzah ya ce daga cikin abubuwan da suka kama akwai bindiga guda biyu, adda 2, motar Toyota Corolla, wayar salula, talabijin guda 4 da kuma injin yankan karfe, daga karshe ya ce za su cigaba da gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna sun samu nasarar kama wasu miyagun masu garkuwa da mutane guda uku da suka dade suna fitinar jama’an jahar Kaduna, tare ceto wata budurwa daga hannunsu.

Mai magana da yawun Yansandan yankin, Mohammed Jilge ne ya bayyana haka ga menema labaru a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu a garin Kaduna, inda yace a ranar Laraba suka samu rahoton an sace wata budurwa yar shekara 22 Hadiza Gambo daga Bungel Ladduga na karamar hukumar Kajuru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng