Yansanda sun kubutar da budurwa daga hannun barayi a Kaduna, sun kama 3

Yansanda sun kubutar da budurwa daga hannun barayi a Kaduna, sun kama 3

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Kaduna sun samu nasarar kama wasu miyagun masu garkuwa da mutane guda uku da suka dade suna fitinar jama’an jahar Kaduna, tare ceto wata budurwa daga hannunsu.

Mai magana da yawun Yansandan yankin, Mohammed Jilge ne ya bayyana haka ga menema labaru a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu a garin Kaduna, inda yace a ranar Laraba suka samu rahoton an sace wata budurwa yar shekara 22 Hadiza Gambo daga Bungel Ladduga na karamar hukumar Kajuru.

KU KARANTA: Amurka ta haramta ma Najeriya mika $100m daga kudin Abacha ga gwamnan jahar Kebbi

“Yan bindiga ne suka yi garkuwa da ita, sa’annan suka arce da ita zuwa wani wuri da ba’a sani ba, nan da rundunar ta tara dakarunta a karkashin jagrancin DPO na Yansandan Kasuwar Magani suka bi sawun yan bindigan.

“Ba tare da jimawa bane jami’an Yansandan suka samu nasarar kama wani Gambo Abubakar dan shekara 57, kuma amsa tambayoyi dangane da satar budurwar, Gambo ya tabbatar da hannunsa cikin sace sacen mutane, daga ciki har da satar mutane biyu a Idon Gida inda suka karbi kudin fansa N1.7m

“Da bincike ya tsananta sai Yansanda suka kama wasu mutane guda biyu Kamal Babawuro da Yahaya Gaiya, wanda ta kai ga an kubutar da Hadiza da ranta, kuma tuni an mikata ga iyalanta.” Inji shi.

Daga karshe ASP Jilge yace a yanzu haka suna cigaba da gudanar da bincike a kan miyagun, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da su gaban kuliya manta sabo don fuskantar hukunci.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar Yansandan Najeriya reshen babban birnin tarayya Abuja sun samu nasarar tarwatsa wasu gungun miyagun yan fashi da makami a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, 21 ga watan Feburairu.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya ta ruwaito an yi musayar wuta tsakanin Yansanda da Yan fashin ne a unguwar Dawaki na Abuja, inda Yansanda suka samu nasarar halaka guda biyu daga cikinsu.

Mai magana da yawun rundunar Yansandan Abuja, Ajuguri Manzah ya sanar da haka a Abuja, inda yace yan fashin sun fuskanci Yansanda ne a daidai inda suka gudanar da fashinsu, wanda hakan ya janyo musayar wuta a tsakanin bangarorin biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel