Bidiyon wata budurwa tana zane mahaifiyarta saboda fasto ya ce mayya ce

Bidiyon wata budurwa tana zane mahaifiyarta saboda fasto ya ce mayya ce

An nadi bidiyon wata mace tana yi wa mahaifiyarta bulala bayan wani fasto ya shaida mata cewa mahafiyarta mayya ce.

A wani bidiyo mara dadin gani da wani mai amfani da shafin sada zumunta mai suna Sam Ituama ya wallafa, an gano matar tana zane mahaifiyarta da bulala a bainar jama'a.

A cewar Ituama, fastocin cocin matar ne ya fada mata cewa ta gaza ganin wani cigaba a rayuwarta ne domin mahaifyarta tana yi mata zagon kasa.

DUBA WANNAN: Ba mu maraba da kai a jam'iyyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP

Sam Ituama ya rubuta haka: 

"Wannan yarinyar tana dukan mahaifiyarta yayin da kawayenta ke daukan bidiyo suna dariya saboda fasto ya ce mahaifiyar mayya ce!

"Shin ina wannan duniyan za ta da mu?"

#Manzonnin Afrika sun iya haddasa fitina a tsakanin iyali.

Ga bidiyon abin ban mamakin a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel