Ba mu maraba da kai a jam'iyyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP

Ba mu maraba da kai a jam'iyyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP

Jam’iyyar APC reshen jihar Ekiti ta shawarci tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose da ya goge tunanin komawa jam’iyyar APC daga ransa.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, sakataren yada labarai na jam’iyyar, Ade Ajayi, ya sanar da hakan a Ado Ekiti a ranar Alhamis.

Ya ce jam’iyyar ba bolar zubar da duk wani dan siyasa da ya gaza bane. Ya kara da cewa ba a bukatar Fayose a jam’iyyar kwata-kwata.

Wannan na kunshe ne a takardar da ya saka hannu. Ajayi ya kwatanta jam’iyyar APC din da jam’iyyar mutane masu matukar dabi’a, nagarta da gogewa a siyasa. Don haka ba za ta iya karbar mutane kamar Fayose ba. Fayose bai cancanci zama dan jam’iyyar APC a jihar ba.

Ba mu bakatar ka a jami'yyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP
Ba mu bakatar ka a jami'yyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kano: Kotu tayi watsi da bukatar PCACC na dakatar da Sarki Sanusi

Jam’iyyar ta sanar da hakan ne yayin da take martani a kan wani zargi da ake na wata magana da ta fito daga bakin Fayose. Ya yi ikirarin komawa jam’iyyar APC din matukar shugaban jam’iyyar PDP na jihar ya kasa aiwatar da aiyukan da suka rataya a kansa.

A don haka ne Ajayi ya ce, “Ba ma maraba da shi zuwa wannan babba kuma tsaftataccen gida namu a jihar nan. Zai fi idan ya zauna a PDP dinsa ya ci gaba da barnarsa a maimakon zuwa wannan gidan tarbiyyan da kuma bin doka.”

“Jama’ar jam’iyyar APC na jihar Ekiti sun san me yake kokarin yi kuma suna jan kunnen mutane kamar Fayose da kada ya kuskura ya zo APC don ba bola ba ce.” ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164