Kano: Kotu tayi watsi da bukatar PCACC na dakatar da Sarki Sanusi

Kano: Kotu tayi watsi da bukatar PCACC na dakatar da Sarki Sanusi

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano a ranar Juma’a, tayi watsi da wani rahoto da hukumar koke ta gwamnati da yaki da rashawa (PCACC) ta fitar wanda ke bukatar a dakatar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II har zuwa lokacin da za a kammala bincike a kan watanda da ake zargin yayi da kudin masarautar.

Mai shari’a O. A. Eguwuatu ya ce PCACC ba ta ba Sarkin damar sauraro ba kafin a fitar da rahoton a kan shi, hakan kuwa ya ci karo da dokar adalci.

Sarkin ya maka PCACC, gwamnan jihar Kano da kuma kwamishinan shari’ar jihar Kano din a gaban kotu. Ya bukaci kotun da ta bayyana cewa rahoton da PCACC ta bada na ranar 6 ga watan Yuni 2019 sun ci karo da hakkinsa na sauraro kuma sun take dokar adalci.

Sanusi ya kara da bukatar kotun da tayi watsi da rahoton farkon da ke danganta shi da damfara, almundahana tare da bukatar dakatar da shi.

A yayin amsa bukatar sarkin, kotun ta bada umarnin a biya shi diyyar N200,000, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Kano: Kotu tayi watsi da bukatar PCACC na dakatar da Sarki Sanusi
Kano: Kotu tayi watsi da bukatar PCACC na dakatar da Sarki Sanusi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Barkewar sabuwar cuta a Benue: 'Yan majalisa sun bukaci a kebance dan majalisa mai wakiltar yankin

A ranar Larabar da ta gabata ne babbar kotun jihar Kano din karkashin jagorancin Mai shari’a Sulaiman Na-Mallam ta hana PCACC ci gaba da bincikar Sarkin.

A binciken farko da hukumar ta fitar, ta bukaci a dakatar da sarkin kafin kammala bincikarsa a kan zargin da ake masa na watanda da sama da biliyan 3.5.

Lauyan Sarkin, Suraj Sa’ida, ya mika bukatar hana hukumar ci gaba da bincikar sarkin.

An zargi wannan binciken a matsayin wani yunckuri na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na hukunta Sarkin sakamakon goyon bayan da ya nuna ga Abba Yusuf na jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2019 na gwamnan jihar. Sarkin ya musanta goyon bayan dan takarar jam’iyyar PDP din a yayin zaben.

Ganduje bai tsaya a nan ba, ya kirkiri sabbin masarautu hudu a Gaya, Rano, Karaye da Bichi wadanda suka kasance masu darajar farko kamar masarautar Kano din don durkusar da rinjayen basaraken.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel