Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a tashar motar Jabi da ke Abuja
Gobarar sassafe ce ta tashi a sananniyar tashar motar nan ta Jabi da ke Abuja. Gobarar kuwa ta lamushe shaguna da kadarori masu tarin yawa a tashar motar, kamar yadda jaridar Sahara Reporters suka ruwaito.
Lamarin ya faru ne a sa'o’in farko na ranar Juma’a. An ga masu ababen hawa na tuki a gaggauce don janye ababen hawansu daga inda gobarar ke aukuwa.
Amma kuma, ‘yan kwana-kwana ko kuma masu kashe gobara sun hallara wajen da gobarar ke aukuwa.
Har dai a halin yanzu ba a san abinda ya zamo musabbabin gobarar ba.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Zamfara: Za a koma zaman majalisar jiha a makarantar firamare

Asali: Twitter
Karin bayani na nan zuwa muku...
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng