Bidiyo: Daliban Sakandare sun yiwa Malamin su dukan tsiya a jihar Katsina

Bidiyo: Daliban Sakandare sun yiwa Malamin su dukan tsiya a jihar Katsina

- Wani bidiyo da yake ta faman yawo a shafukan sadarwa ya nuna yadda wasu daliban makarantar sakandare suka yiwa wani malaminsu dukan tsiya

- Makarantar da inda aka dauki bidiyon ba a bayyana ina ne ba, amma ana kyautata zaton jihar Katsina ne

- Malamin ya shiga komar daliban, bayan ya kama wani dalibi da duka, shi kuma dalibin ya fara ramawa, hakan ya sa abokananshi suka shigar masa

Wasu daliban sun dauki doka a hannunsu, inda suka yiwa Malaminsu dan banzan duka a wata makarantar sakandare da ake kyautata zaton ta jihar Katsina ce.

A wani bidiyo da shafin yanar gizo na Linda Ikeji ya wallafa, an ga Malamin sanye da riga shudiya, Malamin da ba a bayyana sunan shi ba, yana hukunta wani dalibinshi namiji.

Amma a lokacin da ya cigaba da dukan dalibin, sai dalibin ya fara kokarin ramawa, Sauran daliban da suke gefe suna kallo sai suka fara taya daya dalibin, inda suka yiwa malamin yawa.

KU KARANTA: Matar da ta zama mataimakiyar shugaban makarantar sakandare daga aikin shara da goge-goge

Sun yiwa Malamin dan karen duka, inda aka hangi sauran dalibai suna tsalle suna ihu da alamun abin yayi musu dadi.

A wani labari da muka kawo muku jiya kuwa, wani mutumi ne ya bantarewa matarsa hakora har guda hudu saboda wani asiri da ya bankado.

Mutumin wanda yake auren matar na tsawon shekaru masu yawa ya gano cewa 'ya'yan da ya kwashe shekaru masu yawa yana daukar nauyinsu wajen ciyarwa da sutura da kudin makaranta duka ba 'ya'yanshi bane.

Hakan ya sanya ranshi ya baci ya dauki hukunci a hannunshi, inda ya fara jibgarta har ta kai ga sai da tayi asarar hakori guda uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel