'Yar shekara 7 ta tara naira miliyan daya da rabi tana biyawa abokanan ta talakawa kudin abinci a makaranta

'Yar shekara 7 ta tara naira miliyan daya da rabi tana biyawa abokanan ta talakawa kudin abinci a makaranta

Emauni Jeanise Manley ta zama marubuciya a lokacin da take da shekara 5 a duniya, kuma ta zama abin kwatance a cikin abokananta ta hanyar taimaka musu

Yarinyar 'yar aji biyu a makarantar Charles County dake Maryland, ta gano cewa yaran da suke aji daya da dama a cikinsu basa iya biyan kudin abinci idan sun fita hutun lokaci, hakan ya sanya ta fara tara kudi a shafin Facebook domin ta taimaka musu.

"Na ga wasu abokanai na suna cin burodi kawai, sai nace ya kamata na nemi taimako na tara kudi na taimaka musu," Mainley ta ce.

Taje ta zauna tayi magana da mahaifiyarta, Rosalynd Manley, inda take gaya mata 'yan ajinsu da yawa basu da kudi a asusunsu, kuma basu da kudin sayen abinci idan sun fito hutun lokaci daga aji, hakan ya saka suke cin abincin daban.

'Yar shekara 7 ta tara naira miliyan daya da rabi tana biyawa abokanan ta talakawa kudin abinci a makaranta
'Yar shekara 7 ta tara naira miliyan daya da rabi tana biyawa abokanan ta talakawa kudin abinci a makaranta
Asali: Facebook

Da taimakon mahaifiyarta wacce ita ma take aiki a makarantar, Manley ta fara neman taimakon mutane a shafin Facebook domin ta samu kudin da za ta taimakawa abokanan nata.

KU KARANTA: Miji ya bantarewa matarshi hakora guda 4 bayan ya gano 'ya'yansu uku da ya wahala yana raino ba nashi bane

Abinda ta rubuta a shafinta na Facebook din shine, "Hello, ni ce Emaunij! Ina neman taimakon ku. Na lura da akwai dalibai irina da basu da kudin sayen abinci mai kyau sai dai su ci burodi idan mun fito hutun cin abinci, hakan ya sanya naji bana jin dadi sosai. Nayi magana da iyayena kuma na nuna musu ina son taimakawa.

"Na sanar da su zan nemi taimako a shafin Facebook domin mutane su taimaka mana mu biya kudin abincin abokanai na. Dan Allah ku taimaka. Duk abinda ya samu ya isa. Burina na sama musu kudin daga nan zuwa karshen watan Janairu, koda 'yan uwana daliban za su fara samun abinci mai kyau daga farkon watan Fabrairu. Duka abinda aka samu zan sanya shi a cikin asusun abinci na makaranta domin abokanai na."

Abinda tayi kokarin tarawa dala dari takwas ne kawai ($800), amma sai gashi ta samu dala dubu hudu da dari takwas ($4,701) a cikin kwanaki 13 kawai. Duk da ta samu wannan nasara Manley ta cigaba da tarawa 'yan ajin nata kudin abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel