Yan sa kai a jahar Borno sun mayar ma Shekau martani cikin sabon bidiyo

Yan sa kai a jahar Borno sun mayar ma Shekau martani cikin sabon bidiyo

Wasu gungun matasa yan sa kai da yan farauta daga karamar hukumar Biu sun yi alkawarin shiga cikin daji domin farauto shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau tare da yi masa yan rago da hannunsu, kamar yadda shugabansu ya tabbatar.

Shugaban yan sa kan wanda bai bayyana sunansa ya bayyana ne a cikin wani bidiyo inda yake zagaye da sauran matasan kungiyar, yana aika ma shugaban Boko Haram, Shekau sako, inda ya kalubalance shi ya fito su yi ido hudu idan ba ga tsoro ba.

KU KARANTA: Rikicin ma’aurata: Lebura ya kashe matarsa da mugun duka a jahar Legas

Wannan bidiyo dai martani ne ga bidiyon da Shekau ya yi jim kadan bayan ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jahar Borno domin jajanta ma al’ummar jahar, inda ya gargadi Buhari kada ya kara shiga Borno, sa’annan ya yi barazanar kashe Minista Sheikh Isa Ali Pantami da wani masanin Boko Haram Bulama Bukarti.

Sakon da shugaban matasan sa kai ya fada shi ne: “Ina neman tsari a wajen Allah daga sharrin shaidan, wannan martani ne ga Shekau, Shekau ya yi barazanar aikata ta’addanci, toh mu matasan Biu muna yaki a ta’addanci.

“Muna farautar Boko Haram matsorata da Shekau, muna tare da Yangora, Civilian JTF da kuma yan baka da yan Hisba, mun fito da shirinmu zuwa dajin Sambisa domin farautar Shekau da yaransa.

“Shekau ka yi ma Buhari maganan banza, toh ka sani Buhari ba tsaranka bane, Buhari ya fi karfinka, Shekau idan ka shirya mutuwa, mu jiranta mu ke, Shekau idan ya ka isa ka fito, na rantse da Allah sai na yanka ka.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira ga al’ummar jahar Borno da su dauki a ranar Litinin mai zuwa, 24 ga watan Feburairu domin neman taimakon Allah Ubangijin talikai dangane da bala’in ta’addanci na Boko Haram.

Zulum ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da ya fitar da kansa a ranar Laraba, 19 ga watan Feburairu, inda yace akwai bukatar a hada kokarin da Sojoji da sauran jami’an tsaro suke yi da neman taimakon Allah a yaki da Boko Haram.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel