Yanzu-yanzu: EFCC ta damke dan tsohon gwamna, Abubakar Audu

Yanzu-yanzu: EFCC ta damke dan tsohon gwamna, Abubakar Audu

Jamian hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC sun damke Muhammed Audu, dan gidan marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Abubakar Audu.

Hukumar ta damkeshi ne kan laifin zamba cikin aminci a ranar Talata, 18 ga watan Febrairu, 2020.

EFCC ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis idan ta bayyana cewa: "An damkeshi ne a ranar Talata, 18 ga Febrairu 2020 kan laifin karkatar da miliyoyin daloli da biliyoyin Naira da aka baiwa hukumar kwallon kafar Najeriya kyauta wajen amfanin kansa."

" Bincike ya bayyana cewa ya yi amfani da kamfanoninsa biyu Mediterranean Hotels Limited da Mediterranean Sports, wajen karkatar da kudaden kuma ya kasa bayani a kansu."

" Za'a gurfanar da a kotu muddin aka kammala bincike."

Saurari cikakken rahoton..

Asali: Legit.ng

Online view pixel