Almajiranci a Arewa: A dau mataki kai iyayen ba 'ya'yan ba - Sarki Sanusi

Almajiranci a Arewa: A dau mataki kai iyayen ba 'ya'yan ba - Sarki Sanusi

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi kira ga gwamnati da ta kafa dokokin kawo karshen rashin adalci. Ya kara da kira ga gwamnati da ta kama duk iyayen da suka tura ‘yayansu bara ko roko.

A yayin martani mai zafi a taron gyaran zamantakewar iyali don habaka kasar nan, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarta a fadar shugaban kasar a ranar Alhamis, ya ce babu dokar da ta ce namiji ya auri mata, ya haihu kuma ya ki daukar dawainiyar yaran.

Ya ce duk mutumin da yasan talaucinsa ya kai ba zai iya kula da iyalinsa ba, to ya fita da kanshi don bara amma a dena tura yara.

Basaraken yayi kira ga gwamnati da ta kama duk iyayen da suka mayar da dansu almajiri a maimakon a kama dan.

Almajiranci a Arewa: A dau mataki kai iyayen ba 'ya'yan ba - Sarki Sanusi
Almajiranci a Arewa: A dau mataki kai iyayen ba 'ya'yan ba - Sarki Sanusi
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Asiri ya tonu: An gano wuraren da ake boye shanun sata a Zamfara

Idan zamu tuna, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce Arewa za ta ci gaba da tarwatsa kanta matukar ba ta sauya daga yadda take ba. Sarkin yayi wannan maganar ne a ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar Kaduna yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Nasir El-Rufai karo na 60.

Sanusi ya ce a matsayin shugaba, maimaita abinda ka tarar ana yi tare da tsammanin za ka banbanta ba dai-dai bane.

Ya kara da cewa, canji zai samu ne a Arewa idan aka fara yin abubuwa mabanbanta. Ya jinjinawa salon gyaran bangaren ilimi na gwamna El- rufai. Ya ce hakan ne kawai zai iya tseratar da Arewa.

"Dai-dai ne idan gwamna ya bi salon da ya tarar na mulki a cewar mutanen Arewa. Amma ba dai-dai bane gaskiya idan ya bi salon da bai kawo wani canji ga yankin. Idan kuwa shugaba ko mai mulki yayi hakan, zamu iya cewa yana daga cikin matsalar yankin nan," Sanusi ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel