Wasu suna kashe kudinsu ne a kan 'hodar iblis' da luwadi, na zabi sayen motoci - Dino Mekaye ya yi 'shagube'
Tsohon mamba mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a majalisar dattijai, Sanata Dino Melaye, ya ce gara ya kashe kudinsa a kan sayen motoci a kan ya kashe su a kan hodar iblis da luwadi kamar yadda wasu ke yi.
Melaye ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta bayan wani mawaki, Speed Darlington, ya soke shi.
Tsohon dan majalisar ya kasance mai alfahari da tutiya da motocin alfarma masu tsada da ya mallaka. A cikin hotunan motocinsa da yake yawan daukan hoto tare da su a garejin gidansa, akwai Rolls Royce, Bentley, Mercedes Bez G Class da Ferrari.
Mawaki Darlington ya nuna mamakinsa a kan tarin motocin da Melaye ya mallaka, inda ya bayyana cewa, "ikon Allah! duba tarin dukiyar da mutum daya ya mallaka don kawai ya taba zama sanata a Najeriya. An yi sa'a bai samu nasarar lashe zaben gwamna ba, sun karya kafarsa yayin zabe. Bai kamata wani mutum da bashi da sana'a sai siyasa ba ya mallaki dukiya mai yawa haka".

Asali: Instagram
Da yake mayar da martani, Melaye ya ce yana sha'awar sayen motoci kuma bai kamata hakan ya zama matsala ga kowa ba.
DUBA WANNAN: An bayyana abinda cire su Buratai zai haifar a Najeriya
"Kowa yana kashe kudinsa ne a kan abinda yake so. Ni burina shine na mallaki motocin kece raini. Masu tsafi suna kashe makudan kudi domin sayen jini. Wasu a kan luwadi suke kashe kudinsu, wasu a kan bokaye, wasu a kan hodar iblis, wasu kuma su je su boye kudinsu a Switzerland," a martanin Melaye.
Melaye, dan jam'iyyar PDP, mamba ne a majalisar dattijai ta 9 kafin kotu ta soke zabena tare da bayar da umarnin sake sabon zabe, wanda ya jam'iyyar APC ta lashe.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng