Ban taba zuwa Asibiti da zan haihu ba - Mai ‘Ya ‘ya 12 da ta haifi ‘Yan 4

Ban taba zuwa Asibiti da zan haihu ba - Mai ‘Ya ‘ya 12 da ta haifi ‘Yan 4

Wata Mata mai shekaru 30 a Duniya ta haifi jerin ‘Ya ‘ya ‘yan hudu a wani Kauye a jihar Kaduna, inda ta bada labarin yadda ta ji a lokacin da ta ke nakuda a gida.

Sunan wannan Baiwar Allah Zainab Hassan, kuma ta haifi Yara har 12 kafin Ubangiji ya kawo mata rabon wadannan jarirai ‘Yan hudu da ta haifa daga karshe.

Wani abin mamaki shi ne Zainab Hassan ta haifi duka wadannan Yara ne a gida ba a gaban Likita ba. Wannan Mata ta ce asibitin da ake zuwaya yi mata nisa sosai.

Zainab Hassan ta shaidawa Jaridar Vanguard cewa sai an yi amfani da jirgin ruwa an ratsa wani tafki, sannan a hau babur kafin a iya zuwa asibiti daga Kauyensu.

KU KARANTA: Ta nemi ta sace Mahaifiyar kawarta saboda ta samu kudi

Duk wadannan tafiye-tafiye da za ayi, su na bukatar kudi kamar yadda ta bayyana. Nisa da wannan dawainiya ta sa wannan Mata Uwar ‘Ya ‘ya 12 ta haihu a dakinta.

Jaridar ta ce Zainab Hassan ta bayyana irin wahala da zafin da ta ji a lokacin da ta ke faman nakuda. Wannan Mata ta ce haihuwar 'yan 4 a gida ya na da wahala.

A cewarta: “Wannan karo na haifi duka ‘Ya ‘ya na hudu a gidan Mijina ba tare da taimakon kowa ba.” Zainab ta ce babu ruwanta da bitar da ake yi wa masu juna biyu.

Abin da wannan Mata ta ke amfani da su shi ne Magungunan gargajiya da aka saba sha a Kauyen. Mijinta, Mohammed Hassan, ya roki gwamnati ta kawo asibitoci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel