Kogi: Kotu ta wanke Musa Wada daga zargin badakalar takardun firamare

Kogi: Kotu ta wanke Musa Wada daga zargin badakalar takardun firamare

‘Dan takarar jam’iyyar hamayya a Kogi, Musa Wada, ya samu nasara a kotu, bayan an wanke shi daga zargin cewa ya yi karya game da takardun shaidan karatunsa.

Alkalin babban kotun tarayya da ke Lokoja, Kogi, ya yi watsi da karar da wani Abraham John ya kawo gabansa. Alkalin kotun ya ce mai karar bai da wata hujjar kirki.

Kamar yadda mu ka samu labari jiya, Abraham John ya na tuhumar Injiniya Musa Wada da cewa ya yi karya game da takardunsa na makarantar firamare da ya gabatar.

John ya fadawa kotu cewa akwai alamar tambaya a kan satifiket din firamare da ‘Dan takarar na PDP ya mikawa hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC.

A dalilin wannan ne ya bukaci kotu ta ruguza takarar da Musa Wada ya yi a 2019. A karshen shari’ar, Alkali bai samu wata hujja da ta gamsar da wannan ikirari ba.

KU KARANTA: Bello ya sadaukar da nasarar da ya samu a zaben Kogi ga tsohuwarsa

Kogi: Kotu ta wanke Musa Wada daga zargin badakalar takardun firamare
Alkali ya tabbatar da sahihancin satifiket din Musa Wada
Asali: UGC

A Ranar Talata, Alkali mai shari’a D. O. Okorowo ya yi kaca-kaca da Abraham John a game da wannan korafi da ya kai gaban kotu mai lamba FHC/ABJ/CS/1078/19.

D. O. Okorowo ya bayyana karar da John ya shigar da cewa takardar banza ce maras ma’ana, bayan da mai tuhumar ‘Dan takarar ya gaza gabatar da wasu hujjoji.

Lauyan da ke kare Musa Wada, Jibrin Okutepa SAN, ya shaidawa kotu cewa an buga katabora sosai wajen shigar da korafin, don haka ya nemi ayi watsi da karar.

Jam’iyyar PDP ta fitar da jawabi bayan wannan hukunci, ta ce wannan shari’ar ta nuna cewa Musa Wada ya cancanci ya rikewa PDP tuta a zaben da yanzu ake kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng