Yan Najeriya sun ce ana biyanku da yawa - Buhari ga yan majalisa

Yan Najeriya sun ce ana biyanku da yawa - Buhari ga yan majalisa

- An kiyasta yan majalisar dokokin Najeriya a matsayin jami’an gwamnati da aka fi tsana a Najeriya

- Hakan ya samo asali ne daga yawan albashi da alawus din da suke karba wanda mutane da dama ke ganin ya yi yawa sosai

- Shugaba Buhari ya fada wa yan majalisar dokokin tarayyar cewa tunanin mutane a kansu bai da kyau

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba, 19 ga watan Fabrairu, ya fada ma mambobin majalisar dokokin tarayya cewa tunanin jama’a a kansu ba mai kyau bane.

Shugaban kasar ya ce yan Najeriya na kallon yan Majalisa a matsayin mutanen da ke samun kudi da yawa ba tare da aiki mai yawa ba.

Yan Najeriya sun ce ana biyanku da yawa - Buhari ga yan majalisa
Yan Najeriya sun ce ana biyanku da yawa - Buhari ga yan majalisa
Asali: Facebook

Ya yi magana ne a majalisar dokokin tarayya lokacin kaddamar da mujallar majalisar wakilai.

Buhari wanda ya samu wakilcin ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya ce samar da mujallar zai sauya tunanin da mutane suke yi kan Majalisar dokoki.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Kwara ya kori shugabannin gidajen watsa labarai 3 a jiharsa

Ya ce mujallar zai ba jama’a damar gyara bayanai da zai goge kallon da ake yiwa majalisa da kuma haskaka kyawawan aikin da yan majalisar ke yi.

A wani labarin kuma mun ji cewa Matasa yan Najeriya dake cikin gajiyar tsarin bayar da tallafi na N-Power sun yi barazanar shiga yajin aiki na dindindin tare da gudanar da gangamin zanga zangar nuna bacin ransu bisa yadda gwamnati ta gaza biyansu albashin watan Janairu.

Sahara Reporters ta ruwaito matsalar rashin samu hakkokin yan N-Power ba sabon abu bane tun bayan zuwa sabuwar ministar shugaban kasa Buhari, Sa’adiya Umar Faruk, inda aka dauke N-Power daga ofishin shugaban kasa ya koma karkashin ma’aikatarta.

Ko a watan Oktobar 2019 ma sai da matasan suka koka sakamakon daukan watanni uku kafin nan suka samu kudadensu, wanda hakan yasa yan Najeriya ke ganin kamar akwai wata makarkashiya da ministar ke yi na ganin ta dakile shirin, a cewar majiyarmu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel