Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane da dabbobi bayan harin da suka kai Neja

Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane da dabbobi bayan harin da suka kai Neja

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai mummunan farmaki a kauyen Madaka da makwabtansa a cikin karamar hukumar Rafi na jahar Neja, a ranar Laraba, 19 ga watan Feburairu.

Daily Trust ta ruwaito a yayin harin da suka kai, Yan bindigan sun yi tarkata mutane da dama tare daruruwan shanu, inda suka yi awon gaba dasu zuwa cikin dazukan dake zagaye da yankunan.

KU KARANTA: Yansanda sun ki karbar cin hancin N700,000 daga hannun barayin shanu a Sakkwato

Rahotanni sun bayyana da misalin karfe 6:30 na safe ne yan bindigan suka shiga kauyuka suna harbe harbe irin na mai kan uwa da wabi, wanda hakan hakan yasa mazauna kauyukan gudun ‘idan baka yi ba ni wuri’.

A haka suka dauke tsawon sa’o’i da dama suna tafka ta’asa a kauyukan wajen kora shanun jama’a tare da kama duk wanda suka ci karo da shi, ba tare da sun samu tirjiya daga wajen kowa ba. Wata majiya ta bayyana cewa yawancin mutanen da aka sace gajiyayyu ne wanda yan bindigan suka yi amfani dasu a matsayin garkuwa.

“Yan bindigan sun nufi Allawa dake cikin karamar hukumar Shiroro, amma dai bamu da tabbacin ko akwai wanda suka kashe ko suka raunata, amma dai mun ga jiragen rundunar Sojin sama suna yawo a sama bayan jama’a sun tsegumta musu halin da ake ciki.” Inji majiyar.

A jawabinsa, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Neja, Alhaji Ahmed Ibrahim Inga ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace sun samu rahoton harin, amma ba shi da cikakken rahoto game da harin.

A wani labarin kuma, Kwamishinan Yansandan jahar Sakkwato, Ibrahim Sani Kaoje ya bayyana yadda wasu gungun barayin shanu suka yi ma jami’an Yansanda tayin kudi N700,000 a matsayin cin hanci domin su basu daman tserewa.

Ka’oje ya bayyana haka ne yayin da yake baje kolin mutane 19 da suka kama da laifin satar shanu, fashi da makami, fyade da kuma kasancewa mambobin wata muguwar kungiya dake garkuwa da mutane.

Kwamishinan yace mutane 9 daga cikin garin Sakkwato ne suka kai ma Yansanda karar wasu mutane shida da suke zargi da satar shanunsu, inda ya bayyana sunayensu kamar haka; Abubakar Mamuda, Aliyu Shehu, Yunusa Tukur, Alisa’u Abdullahi, Wadata Shehu da Aminu Muktar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel