Yansanda sun ki karbar cin hancin N700,000 daga hannun barayin shanu a Sakkwato

Yansanda sun ki karbar cin hancin N700,000 daga hannun barayin shanu a Sakkwato

Kwamishinan Yansandan jahar Sakkwato, Ibrahim Sani Kaoje ya bayyana yadda wasu gungun barayin shanu suka yi ma jami’an Yansanda tayin kudi N700,000 a matsayin cin hanci domin su basu daman tserewa.

Daily Trust ta ruwaito Ka’oje ya bayyana haka ne yayin da yake baje kolin mutane 19 da suka kama da laifin satar shanu, fashi da makami, fyade da kuma kasancewa mambobin wata muguwar kungiya dake garkuwa da mutane.

KU KARANTA: Cigaban ilimi: BUK ta kaddamar da gidan talabijin da rediyo a jahar Kano

Kwamishinan yace mutane 9 daga cikin garin Sakkwato ne suka kai ma Yansanda karar wasu mutane shida da suke zargi da satar shanunsu, inda ya bayyana sunayensu kamar haka; Abubakar Mamuda, Aliyu Shehu, Yunusa Tukur, Alisa’u Abdullahi, Wadata Shehu da Aminu Muktar.

Kwamishinan ya bayyana cewa mutanen 6 sun hada baki da Abdulrasheed Shanau, Taju Mohammed, Tukur Abubakar da Kabiru Bauri wajen kai farmaki zuwa gidajen mutanen da suka kai ma Yansanda kara suka kwashe shanunsu da tumakai, sa’annan suka zubasu a wata mota mai lamba AA 344 BLE Sakkwato.

“Da bincike ya natsa, mutanen sun amsa laifinsu, kuma sun bayyana sun sace dabbobin ne daga karamar hukumar Bodinga da karamar hukumar Dange/Shanu. Sa’annan sun yi ma Yansanda tayin N700,000 a matsayin cin hanci don su basu daman tserewa, amma Yansanda suka ki, kuma suka kamasu.” Inji shi.

Kwamishinan yace sun kama shanu 11, tumaki 24, da akuya 8 sai kuma babura guda 3. A wani labarin kuma, kwamishinan yace a ranar 11 ga watan Feburairu sun kama wata mota a Kwanawa yayin da suke binciken ababen hawa, inda fasinjojin motar suka tsere.

Sai dai da suka bincike motar sai suka tarar da bindigun AK 47 guda hudu a boye, don haka yace suna nan sun baza komarsu don ganin sun kamo mutanen. Daga karshe yace sun kama wani Samaila Mamman dake baiwa barayin mutane bayanan sirri a jahar Sakkwato.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel