EFCC ta dakile yunkurin shigar wa da mai laifi miyagun kwayoyi
Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta damke wani mutum mai shekaru 60, Muyiwa Otuyola, yayin da yake kokarin safarar kwaya ga dansa, Damilola Otuyalo, da aka tsare a ofishin hukumar da ke Ibadan, jihar Oyo.
A cewar jawabin da ofishin EFCC reshen jihar Oyo ya fitar ranar Talata, an bayyana cewa wani jami'in hukumar ne ya kama mutumin dumu - dumu a daidai lokacin da yake mika wa dan nasa kunshin miyagun kwayoyi yayin da ya ziyarce shi ranar Litinin.
Jawabin ya kara da cewa, jami,in ya ankarar da abokan aikinsa kuma an samu nasarar kwace kwayoyin. Wata ma'aikaciyar sashen lafiya a hukumar EFCC, da ta duba kwayoyin, ta bayyana cewa kwayar 'Rophynol' ce a cikin kullin da aka kama Muyiwa ya kai wa Damilola.
Ana amfani da kwayar 'Rophynol' bisa umarnin likita ga masu larurar fama da matsananciyar mantuwa ko kuma don saka marasa lafiya bacci kafin a yi musu tiyata.
EFCC ta bayyana cewa ta kama Damilola ne bisa zarginsa da safarar kudi zuwa kasar Ingila. Rundunar 'yan sandan kasar Ingila ne suka fara bayyana nemansa ruwa a jallo bayan binciken badakalar wasu kudade da yawansu ya kai £500,000.
DUBA WANNAN: Daraja: Kasashe 8 da takardun Naira za su mayar da mutum tamkar Sarki
Hukumar ta ce hukumomin tsaron kasashen ketare sun dade suna neman Damilola ruwa a jallo kafin daga bisani a kama shi a Najeriya.
A cewar jawabin, EFCC ta ce zata mika mahaifin Damilola hannun hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da zarar ta kammala bincike a kansa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng