Zulum ya yi kira ga jama’an Borno su dauki azumi a ranar Litinin don neman taimakon Allah

Zulum ya yi kira ga jama’an Borno su dauki azumi a ranar Litinin don neman taimakon Allah

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi kira ga al’ummar jahar Borno da su dauki a ranar Litinin mai zuwa, 24 ga watan Feburairu domin neman taimakon Allah Ubangijin talikai dangane da bala’in ta’addanci na Boko Haram.

Zulum ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da ya fitar da kansa a ranar Laraba, 19 ga watan Feburairu, inda yace akwai bukatar a hada kokarin da Sojoji da sauran jami’an tsaro suke yi da neman taimakon Allah a yaki da Boko Haram.

KU KARANTA: Ta’addanci: Boko Haram ta kashe malaman makaranta 547 a yankin Arewa maso gabas

Zulum ya yi kira ga jama’an Borno su dauki azumi a ranar Litinin don neman taimakon Allah
Zulum ya yi kira ga jama’an Borno su dauki azumi a ranar Litinin don neman taimakon Allah
Asali: Facebook

Ana samun yawaitan hare haren Boko Haram a yan kwanakin nan, inda ko a ranar Talata sai da suka kaddamar da mummunar samame a karamar hukumar Chibok inda suka yi ta’adi sosai ba kadan ba.

Gwamnan yace duk dai Sojoji na aiki, ana sayen musu makamai, kuma su ma gwamnatin jaha sun tura Sojojin sa kai, yan banga da maharba da dama zuwa wurare daban daban don yaki da ta’addanci, amma jama’a da dama sun yi kira da ya kamata kowa ya dauki azumi don neman agaji daga Allah.

“Na san wannan zai zama kamar sabon abu, amma jahar Borno ta dade tana fama da sabon abu tun a shekarar 2009, kuma wasu lokuttan, sababbin matsaloli suna bukatar sababbin dabarun magance su ne.

“Don haka a matsayina na gwamnanku, na sanar da ranar 24 ga watan Feburairu a matsayin ranar azumi, zan dauki azumi a wannan rana, kuma ina kira ga jama’an Borno wanda zai iya shi ma ya dauki azumin, haka zalika ina kira ga sauran abokan jahar Borno su taya mu da wannan azumi don neman Allah Ya taimakemu.” Inji shi

Haka zalika Zulum yace Shehun Borno ma ya bashi tabbacin umartar dukkanin malamai da limamai dake fadin jahar zasu gudanar da Al-Qunut a duka salloli biyar na ranar Litinin, su ma shuwagabannin kiristoci zasu gudanar da addu’o’i na musamman a ranar.

Daga karshe Zulum ya tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na da kyakkyawar niyya wajen yaki da ta’addanci, don haka ya nemi a saka shi a cikin addu’a, Sojoji dake bakin daga da kuma wadanda suka mutu da ma wadanda suka bace, har da wadanda suka jikkata a dalilin ta’addanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel