Yan bindiga sun sace fasinjoji 12 a Kogi, sun bukaci a biya miliyan 1.8 kan kowani mutum guda

Yan bindiga sun sace fasinjoji 12 a Kogi, sun bukaci a biya miliyan 1.8 kan kowani mutum guda

- Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 12 a wata motar kasuwa yayinda suke a hanyarsa na zuwa Kogi daga Warri a jahar Delta

- An yi garkuwa da fasinjojin ne a tsakanin Itobe da Ajegu a karamar hukumar Ofu da ke jahar Kogi

- Masu garkuwan sun bukaci a biya kudin fansar kowani mutum guda naira miliyan 1.5

Wani rahoto daga jaridar Vanguard ya nuna cewa an yi garkuwa da mutane 12 a hanyar garin Itobe-Ajegu da ke karamar hukumar Ofu na jahar Kogi.

A cewar rahoton, lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Fabrairu.

Wata majiya ta rahoto cewa masu garkuwan sun bukaci kudin fansa naira miliyan 30 domin su saki mutanen.

Yan bindiga sun sace fasinjoji 12 a Kogi, sun bukaci a biya miliyan 1.8 kan kowani mutum guda
Yan bindiga sun sace fasinjoji 12 a Kogi, sun bukaci a biya miliyan 1.8 kan kowani mutum guda
Asali: Facebook

Fasinjojin na tafiya ne a wata motar bas na kasuwa daga Warri a jahar Delta zuwa Anyigba a jahar Kogi dauke da fasinjoji 16.

An tattaro cewa motar ta shigi masu garkuwa da mutanen ne a tsakanin Itobe da Ajegu da ke karamar hukumar Ofu.

Wata majiya wacce ta bayyana cewa masu garkuwan wadanda a baya suka bukaci a biya naira miliyan 30 kudin fansa, a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu sun rage kudin zuwa naira miliyan 1.5 kowani mutum guda inda ya kama naira miliyan 18 gaba daya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a hukumar NDDC (jerin sunaye)

Kakakin yan sandan jahar Kogi, DSP William Ayah, ya tabbatar da lamarin.

A wani labarin kuma, mun ji cewa ayin da rashin tsaro ya ke cigaba da dabaibaye Najeriya, shugaban majalisar wakilan kasar ya na cigaba da neman gudumuwa da taimakon kasashen ketare.

Mai girma Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya roki kasar Sin watau China da ta kawowa gwamnatin Najeriya agaji domin ta magance matsalolin da kasar ke ciki.

Shugaban majalisar wakilan tarayyar ya gabatar da kokon bararsa ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadar kasar ta Sin a Najeriya, Mista Zhou Pingjian.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel