Coronavirus: Jackie Chan zai bada N48.7 ga wanda ya kirkiro maganin cuta

Coronavirus: Jackie Chan zai bada N48.7 ga wanda ya kirkiro maganin cuta

Cutar Coronavirus ta na cigaba da kashe Bayin Allah a Duniya. Kusan har yanzu an rasa gano sirrin yadda za a yaki wannan muguwar cuta da ta addabi jama’a.

A dalilin haka, fitaccen ‘Dan wasan kwaikwayon nan, Jackie Chan, ya sa kudi har fam miliyan R2 ga wanda ya iya samo maganin wannan cuta da ta barke a kasashe.

A kudin Najeriya wannan kudi na ladan bincike da za a ba duk Masanin da ya yi nasarar bankado maganin cutar ta Coronavirus a Duniya sun kai N48, 768, 880. 00.

Rahotanni sun bayyana cewa Tauraro Jackie Chan zai bada kudi Yuan miliyan guda ne ga duk wanda bincikensa ya kai ga iya gano maganin da zai warkar da cutar.

Kawo yanzu, cutar da ta fara bayyana a Garin Wuhan da ke cikin kasar Sin ta ci mutane 1400. Haka zalika akwai mutane fiye 60, 000 da ke dauke da cutar a yanzu.

KU KARANTA: Najeriya ta nemi China ta taimaka mata a kan harkar tsaro

Jaridar The Star ta fitar da rahoto cewa Jackie Chan ya ce zai yi kokari wajen ganin Jama’a sun rabu da wannan cuta ta hanyar saka tukwuici ga manyan masu bincike.

Domin tabbatar da kokarin da ya ke yi, Chan ya ce:“Ko wace kungiya ko mutumi ya iya gano maganin cutar, ina so in yi masu godiya, kuma in ba sa yuan miliyan daya.”

Sharararen ‘Dan wasan kwaikwayon na Duniya ya nuna cewa ba don kudi ya ke so ayi wannan bincike ba, sai dai don ya ceci mutanensa daga kamuwa da annobar.

‘Dan wasan ya koka game da yadda annobar ta rutsa da Bayin Allah da-dama har kuma ta yi sanadiyyar mutuwarsu. Kusan cutar ta fi karfi a Yankin Asiya da Turai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel