Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a hukumar NDDC (jerin sunaye)

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a hukumar NDDC (jerin sunaye)

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sauye-sauye a kwamitin wucin gadi na hukumar ci gaban Niger Delta (NDDC)

- Baya ga sauyin da ya yi, shugaba Buhari ya kuma nada sabon mukaddashin daraktan hukumar

- Pondei ya maye gurbin Barr Joy Nunieh a yanzu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tsarin kwamitin wucin gadi na hukumar ci gaban Niger Delta (NDDC).

Buhari ya maye gurbin Barr Joy Nunieh da Farfesa Kemebradikumo Pondei a matsayin mukaddashin manajan darakta na hukumar.

Shugaban kasar ya kuka kara yawan mambobin kwamitin daga mutum uku zuwa biyar.

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a hukumar NDDC (jerin sunaye)
Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci a hukumar NDDC (jerin sunaye)
Asali: UGC

Sauran mambobin kwamitin sune;

1. Dr Cairo Ohougboh, Mukaddashin daraktan ayyuka

2. Mista Ibanga Bassey Etang, Mukaddashin daraktan kudi da gudanarwa

3. Misis Caroline Nagbo, mamba

4. Cecilia Bukola Akintomide, OON, wacce ta kasance tsohuwar mataimakiyar shugaban bankin ci gaban Afrika a matsayin mamba.

A wani labari na daban, mun ji cewa a yayin da rashin tsaro ya ke cigaba da dabaibaye Najeriya, shugaban majalisar wakilan kasar ya na cigaba da neman gudumuwa da taimakon kasashen ketare. Mai girma Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya roki kasar Sin watau China ta kawowa gwamnatin Najeriya agaji domin ta magance matsalolin da kasar ke ciki.

Shugaban majalisar wakilan tarayyar ya gabatar da kokon bararsa ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jakadar kasar ta Sin a Najeriya, Mista Zhou Pingjian.

Femi Gbajabiamila ya nemi alfarma wajen kasar Sin ta hannun Jakadanta, inda ya shaida masa da cewa rashin tsaro ne babbar matsalar Najeriya a halin yanzu.

Honarabul Gbajabiamila ya ce: “Babbar matsalar mu a halin yanzu ita ce matsalar rashin tsaro, kuma za mu yi murna mu samu taimako yanzu daga gare ku.”

KU KARANTA KUMA: Kudin diyar Ibro: Afakallah zai yi maka Baban Chinedu a kotu

Kakakin majalisar wakilan ya shaidawa Zhou Pingjian cewa gwamnatin Najeriya za ta yi farin-ciki da kowane irin taimako ta samu daga kasarsa a halin da ake ciki.

Jaridar Daily Trust ta ce Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi wannan rokon alfarma ne a Ranar Talata, 18 ga Watan Fubrairun 2020 lokacin da ya hadu da Jakadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel